Jami’ar Aliko Ɗangote ta yaye ɗalibai 18,000 tare da karrama wasu manyan mutane

Spread the love

Daga ABUBAKAR M TAHEER

Jamiar kimiyya da fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil ta yaye ɗalibai 18,000 a karo na 5 bayan shafe tsawon lokaci ba tare da gudanar da taron ba.

Taron daya gudana a ɗakin taro na jami’ar ya samu halarta mashahuran mutane irinsu Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Aliko Ɗangote, Ɗahiru Barau Mangal,Alhaji Mustapha Ado Muhammad, Dr Ahmad Adeniyi Raji, Femi Odetola da sauran su.

Haka kuma an samu halarta shuwagannin jamioin daban-daban daga faɗin kasar nan.

Da yake jawabi Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cigaba da bada goyon bayan gwamnatinsa wajen haɓaka harkar koyo da koyarwa na jimi’ar tare da alƙawarin cigaba da kula da jin daɗin malaman jami’ar.

A nasa jawabin Shahararren ɗan Kasuwa wanda jami’ar taci sunansa Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cigaba da bada tallafi ga jami’ar kamar yadda ya saba.

Cikin wani shiri wanda Ɗangote ya kira shi da Development Plan nan da Shekaru biyar, Ɗangote ya bayyana cewa gidauniyarsa za ta kashe Naira biliyan 15 wajen gudanar da ayyuka irinsu Sabin ɗakin kwanan ɗalibai, ɗakin gwaje-gwaje na zamani, ɗakin kwamfutoci na zamani, gyara zauren sanate na jimi’ar da kuma tsarin kula da ɗalibai masu hazaƙa bayan sun kammala hidimar ƙasa.

A nan take Alhaji Aliko yayi alƙawarin ɗaukar aiki ga duk ɗaliban da suka zama masu hazaƙa a shekararsu.

Haka kuma jami’ar ta bada shaidar digirin girmamawa ga wanda ya ƙirƙiri jami’ar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, Femi Odetola, Alhaji Mustapha Ado Muhammad, Dr Ahmad Adeniyi Raji SAN.

Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga hukumar jami’ar bisa wannan karramawa da suka masa wanda hakan ya samo asali ne daga ƙoƙarinsa wajen ciyar da ilimi gaba a jihar Kano.

Haka kuma jami’ar ta karrama ɗalibai masu hazaƙa da lambobin yabo wanda suka fito daga tsangayoyin ilimi daban-daban dake jami’ar.

Alhaji Barau Mangal ya yi alƙawarin gado 500 a ɗakin kwanan ɗalibai maza, Alhaji Mustapha Ado Muhammad shima gado 500 a ɗakin kwanan ɗalibai mata, Dr. Ahmed Adeniyi Raji SAN ya bada kyautar miliyan da gidajen malamai, sai Femi Odetola ya bada gado 500 wanda kimarsu ta kai Miliyan 500.

Da yake jawabin godiya Shugaban jami’ar Farfesa Musa Tukur yakasai ya bayyana farin cikinsa kan wannnan lamari tare da fatan alkairi ga mahalarta taron da suka zo daga sassa daban-daban na faɗin kasar nan.

By ukarofi