‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 200 bisa aikata laifuka daban daban da suka haɗa da ta’addanci da fashi da makami cikin watan da ya gabata.
Jami’in huɗɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar sadiq Aliyu ya bayyana haka a hira da manema labarai a ofishin sa.
Ya sanar da cewa jami’an ‘yan sandan sun Kama ‘yan ta’adda guda 15 tare da ceto mutane 130 da dabbobi guda 174 a watan da ya wuce.
Haka kuma ‘yan sandan sun kama mutane da ake zargi da fashi da makami su 25 da kuma waɗanda ake zargi da kisan kai su 30.
Jami’an tsaron sun gano haramtattun ƙwayoyi masu sa maye da suka haɗa da D5 guda 55 da buhun tabar wiwi guda 78 tare da ƙwayar Tramdol leda takwas.
Har ila yau ‘yan sanda sun gano mota guda ɗaya da babura guda biyu da ake zargi na sata ne,sai kuma bindiga ƙirar gida guda biyu.
DSP Abubakar sadiq ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda a jihar CP Bello Shehu ya yabawa gwamnatin Katsina da al’ummar jihar bisa goyon baya da suke baiwa rundunar.
Yace babu shakka wannan irin gudunmawa ya taimakawa rundunar wajan samun nasarar gudanar da aikin su.
Kwamishinan sai yayi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da ba ‘yan sandan jihar goyon baya ta basu bayanan sirri na wajan maɓoyan ɓata gari.
CP Bello Shehu ya jaddada ƙudirin rundunar sa na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.
