
Daga BELLO A. BABAJI0
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin kawo gyara a fannin raba wutar lantarki a sassan kasar, inda ta fara da kamfanoni biyu da ayyukansu suka gaza.
Hakan ya biyo bayan nazari game da kalubalen da da kamfanonin na DisCos suke fuskanta, waɗanda suka hada da nisan alaka da gwamnati da samun wadatattun kayan aiki da rashin karfi ta fuskar kudaden gudanarwa.
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana shirin bayan kammala zama da wakilan Hukumar Ķasa-da-kasa ta ƙasar Japan, wadda ta gabatar da tsarin yadda za a shawo kan matsalolin fannin raba wutar lantarki a Nijeriya.
Ya ce, daga yanzu ba za su zura wa kamfanonin da ba sa yin ayyukansu yadda ya dace ido ba domin za su yi amfani da hukumar gudanarwa wajen sabonta tsarin ire-iren kamfanonin.
Za a fara aiki ne da tsarin, wanda aka yi wa lakabi da ‘Pilot Scheme’ a tsakanin watan Mayu da Agustan 2025, kuma zai mayar da hankali ne kan kamfani daya a Arewa da daya a Kudu.
A baya ne dai Ministan ya yi ta jaddada damuwa akan rashin zuba jari a harkokin raba wuta daga kamfanonin lantarki a Nijeriya.
Ya bayyana hakan a matsayin abinda ke hana samun ci-gaban manufofin gwamnati musamman duba da yadda aka kara kudin wuta ga kwastomomin lantarki.
