Karrama Kwankwaso da Jami’ar Ɗangote ta yi da digirin girmamawa an yi abin da ya kamata – Hon. Nura Dala 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Babban hadimi na musamman ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Hon. Nura Maiƙarfi Dala ya bayyana karramawar da jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko ɗangote ta yi wa jagoran kwankwasiyya  Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da digirin girmamawa da cewa  an yi abinda ya kamata.

Ya ce ba shi digirin girmamawar tabbas an ajiye kwarya a gurbinta ne, idan aka yi la’akari da irin gudummuwa da ya bai wa jihar Kano musamman a harkar ilimi.

Hon. Nura Maiƙarfi Dala ya yi nuni da cewa su ma waɗanda jami’ar ta karrama da suka haɗa da shugaban kamfanin AMASCO Alhaji Mustapha Ado da Alhaji ɗahiru Barau Mamgal da Alhaji Aliko ɗangote a matsayin uban Jami’ar mutane ne  da Allah ya horewa arziki suke yin hidima ga al’umma, ya roki Allah ya yawaita irinsu sannan kuma ‘yan baya da suke tasowa su yi koyi da su wajen bada gudummuwa ga cigaban al’umma.

Ita ma Hajiya Rahana Iliyasu mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso shawara kan harkokin mata ta ce duk ɗaukaka da Dakta Rabiu Musa ke samu daga Allah ne saboda irin kishinsa da son cigaban al’umma musamman talakawa, don haka yake ta samun ɗaukaka.

Da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Shehu Tijjani mai kula da ofishin Sanatan Kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga ya ce waɗanda aka karrama tun daga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Aliko ɗangote da ya zama shugaban jami’ar da Alhaji Mustapha AMMASCO da ɗahiru Mangal suna bada matuƙar gudummuwa wajen tallafawa cigaban ilimi.

By ukarofi