Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa dakataccen gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya kai masa ziyara a kwanakin baya domin neman sulhu a cikin rikicin siyasar da ke tsakanin shugabannin biyu.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ne ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan rahotannin da ke cewa Fubara, wanda aka dakatar a baya, ya ziyarci ministar babban birnin tarayya Abuja.
“Eh, ya ziyarci ni,” inji Wike yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Ya ƙara da cewa, “Ya zo min da gwamnoni biyu da dattijon jiha ɗaya, duk gwamnonin APC ne, ya ce yana son a yi sulhu.”
A cewar majiyoyin da ke da masaniya a taron, waɗanda Fubara ya zo da su sun haɗa da gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ebonyi Francis Nwifuru, da tsohon gwamnan Ogun Olusegun Osoba.
An bayar da rahoton cewa sun shiga gidan Wike ba tare da wata turjiya ba, lamarin da ke nuni da cewa sun daɗe da sabawa tsakanin abokan hamayyar siyasar biyu.
Wata majiya ta ce, “Fubara ya shiga cikin falon Wike kai tsaye saboda wannan sanannen wuri ne a gare shi,” yana mai bayyana ƙawancen siyasar da suka yi a baya, wanda tun daga lokacin ya koma cikin gwagwarmayar mulki.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Fubara, mataimakinsa, Farfesa Ngozi Odu; da ’yan majalisar jiha na tsawon watanni shida.
Tinubu ya kuma kafa dokar ta-ɓaci a jihar Ribas yayin da ya naɗa shugaban hukumar sole, shugaban sojojin ruwa, Ibok-Ete Ibas mai ritaya.
Dakatarwar dai wani mataki ne da shugaban ƙasar ya ɗauka domin hana ɓarkewar rikicin siyasa a jihar Ribas.
Rikicin jihar Ribas dai ya samo asali ne sakamakon takun saƙa tsakanin Fubara da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.
Mutanen biyu dai na fafatawa ne don ganin sun mallaki ikon siyasa a jihar, lamarin da ya kusan rikiɗewa ya haifar da matsalar tsaro, biyo bayan barazanar da tsagerun Neja Delta suka yi na kai hari a cibiyoyin mai a jihar.
