
Daga BELLO A.BABAJI
A cigaba da nuna kishin ƙasa da jajircewar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, Shugaba Tinubu ya gana da shuwagabannin tsaro na ƙasar inda ya ƙarfafe su wajen kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya.
Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cikakken rahoto bayan taron gaggawa da Shugaban Ƙasa ya jagoranta, inda manyan hafsoshin tsaro da sauran jami’an tsaro suka halarta.
Janar Musa ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa na matuƙar damuwa da yadda barazanar tsaro ke ƙara ƙarfi, musamman sakamakon matsin lamba daga kungiyoyin jihadi da ta’addanci da ke yaduwa a yankin Sahel. Ya bayyana cewa wannan lamarin ne ke ƙoƙarin kutsowa cikin Najeriya ta hanyar iyakokinmu da ke da buɗaɗɗar hanya. Amma cikin tsare-tsare masu ma’ana, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni kai tsaye da nufin ƙara ƙarfin rundunonin tsaro da kuma haɗa kai da ƙasashen da ke makwabtaka da mu don magance wannan barazana.
Baya ga haka, Janar Musa ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa ya bayar da amincewa kan sayen sabbin kayan aikin tsaro, musamman jiragen yaki da sauran kayan aikin zamani, da kuma ƙarawa rundunoninmu ƙarfi. Ya jaddada cewa ba kawai ana dogaro da bindiga da farmaki ba, a’a, ana ɗaukar hanyoyin da ba na amfani da ƙarfi ba domin magance rashin tsaro ta hanyar kawo ci gaba a cikin al’umma.
A cikin jawabin nasa, Janar Musa ya ce gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi suna da rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, domin tsaro aiki ne na kowa da kowa. Ya bayyana cewa an riga an fara aiki kafada da kafada da gwamnonin jihohi, inda ya bayyana ziyarar da suka kai Maiduguri da sauran jihohi a Arewa maso Gabas a matsayin misali na irin wannan haɗin kai.
Ya kuma buƙaci ’yan ƙasa da su rika bayar da goyon baya ga jami’an tsaro da kuma gujewa yada labaran ƙarya da bidiyon bogi da ke nufin jefa ƙasa cikin rudani.
“Idan Najeriya ta ruguje, ba wanda zai tsira. Don haka wajibi ne mu ɗaure mu haɗa kai don kare ƙasarmu daga maƙiyan da ke ƙoƙarin hana ci gaba da zaman lafiya.” Inji Shi.
A ƙarshe, Janar Musa ya bayar da tabbacin cewa rundunonin tsaro a karkashin wannan gwamnati za su ci gaba da yin nasara, ba tare da gajiyawa ba. Ya ce masu yi musu mugun fata waɗanda ke raina kokarin gwamnati za su ci gaba da jin kunya domin nasara za ta ci gaba da bayyana a fili.
