
Daga BELLO A. BABAJI
Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa al’umma cewa sojoji na aiki tuķuru domin shawo kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a baya-bayan nan.
Ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin samar da ƙarin kayan aiki musamman na sama domin ƙarfafa yaƙi da ƴan tada ƙayar-baya da ake yi.
Janar Musa ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaban ƙasar ya yi da manyan hafsoshin tsaro a Fadarsa da ke Abuja, ranar Juma’a.
Ya kuma ce, tuni aka sayo kayan yaƙin domin daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka zafafa kai hare-hare a ƴan watannin nan, musammman a yankin arewa maso gaba.
“Shugaban ƙasa ya bada umarnin abu na gaba da za a yi, da kuma haɗa-kai da sauran ƙasashe da muke makwabtaka da su saboda yanayin wurarensu ne ke ƙara rura wutar wannan lamari a ƙasar mu” in ji Janar Musa.

Ya kara da cewa, an ƙara ƙarfafa rundunoni tare da sayan makamai domin ganin an magance matsalar da aka daɗe ana fama da ita a sassan daban-dabanna ƙasar.
“Shugaban ƙasa na kuma duba yiwuwar tattaunawa da gwamnoni domin samun goyon bayansu ta hanyar tabbatar da cewa al’umma sun mori ribar dimokraɗiyya da kuma kakkaɓe ayyukan ƴan ta’adda”, inji shi.
BBC Hausa ta ruwaito cewa, Babban hafsan tsaron ya alaƙanta ƙaruwar rashin tsaro a Nijeriya da ƙara ƙaimi da ƴan ta’dda da kuma masu ikirarin jihadi ke yi a faɗin yankin Sahel, inda ya ce abin da ya sa ƙasar ke cikin matsin lamba shi ne rashin kyawun yanayin iyakokinta.
