Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar Crystal Palace ta kafa tarihi bayan da ta doke Manchester City da ci 1-0 a wasan ƙarshe na FA Cup da aka buga a filin wasa na Wembley. Wannan ne karo na farko da ƙungiyar daga kudancin London ta lashe babban kofi cikin shekaru 120 da kafuwarta.
Ɗan wasan gaba Eberechi Eze ne ya zura ƙwallon nasara a minti na 16 da fara wasa.
Manchester City ta samu damar farkewa a minti na 33 bayan da aka basu bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma Dean Henderson ya hana Omar Marmoush cin ƙwallon.
A minti na 58, Daniel Muñoz ya ƙara jefa kwallo a raga, amma alƙalin wasa ya soke ta saboda dokar satar gida (offside).
Koci Oliver Glasner da tawagarsa sun kasance ‘yan gaba da kura a wasan, ganin yadda Man City ke da ƙwarewa, duk da cewar kakar bana ta firimiya ba ta musu daɗi ba.
Wannan nasara ta zama kofi na farko tun da suka lashe Full Members’ Cup a kakar 1990/91, kuma shi ne kofi na farko a tarihin ƙungiyar cikin shekaru 164 da kafuwa.
Sakamakon haka, Crystal Palace ta samu gurbi kai tsaye a zagayen rukuni na gasar UEFA Europa League ta kakar wasa mai zuwa.
