Ilimin boko tsani ne ga cigaban rayuwa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A makon da ya gabata, kafafen watsa labarai musamman a nan Arewa sun rawaito cewa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ƙauran Bauchi, ya furta wasu maganganu da ake dangantawa da kalamai masu haɗari ga cigaban ilimi. Kalaman da Gwamnan ya faɗa dai an samu ne daga wani bidiyo da aka naɗa a wajen bikin yayen wasu matasa da suka kammala koyon sana’o’i.

Wannan bidiyo wanda jama’a suka yi ta yaɗa shi a zaurukan sada zumunta, musamman a manhajar Instagram, daga inda aka ce wannan bidiyo ya samo asali, ya haifar da muhawara mai zafi. Jaridar Politicsnigeria ta rawaito cewa, an jiyo gwamnan yana cewa, ‘Ba lallai ne sai mutum ya yi ilimin boko zai samu arziƙi ko ɗaukaka a rayuwarsa ba.’

Cikin jawaban da ya yi, Bala Mohammed ya bayyana cewa, ilimin boko wata hanya ce guda ɗaya wacce ba lallai ne kowa sai ya bi ta, kafin a ce masa mai ilimi, ko kafin ya samu nasarori a rayuwarsa ba. Ya kuma bayyana musu muhimmancin riƙo da sana’a da kasuwanci, waɗanda su ne sana’o’in da mutanen baya suka dogara da su, har ma kuma suka samu arziƙi mai yawa. Ya ce, ko shi ma da haka ya fara, kuma yau ga matakin da yake.

A tawaice dai, Gwamnan Jihar Bauchi na magana ne da nufin ƙarfafa gwiwar matasa su nemi sana’a, su bar sa rai kan ilimin boko da samun aikin gwamnati, wanda samunsa bashi da tabbas. Sai dai yadda jama’a suka kalli wancan jawabi nasa na kallon kamar ya ƙasƙantar da ilimin boko ne a wajen waɗannan matasa, waɗanda za su iya samun nasarori masu yawa daga ilimin bokon idan da shima sun riƙe shi da kyau. Amma a yadda ya nuna kamar bokon ba shi da wani muhimmanci a rayuwar su, da yin sa da barin sa duk ɗaya ne.

‘Yan boko da manazarta da dama sun yi tsokaci game da waɗannan kalamai na Gwamnan, tare da yin Allah wadai da ire-iren waɗannan kalamai, da suke ganin suna daɗa dakushe karsashi da cigaban ilimi a zukatan al’ummar Arewa. A yayin da a gefe guda ake kuka da komabayan da Arewa ke fuskanta kan taɓarɓarewar ilimi. Kabiru ɗanladi Lawanti, ɗan jarida kuma malamin jami’a ya nuna rashin dacewa kan maganganun da wasu ’yan Nijeriya ke yi, akan muhimmancin ilimin boko, inda har wasu ke auna ilimin boko da sana’a.

Ya ce, babu inda koyon sana’a yake daidai da karatun boko ko ilimin digiri. Bilhasali ma sai dai a ce ilimin boko yana ƙarfafa yadda ake tafiyar da sana’o’i. Ilimin boko hanya ce ta samun sana’a da ayyukan yi, da inganta tafiyar da harkokin rayuwa. Ilimin boko a karan kansa shi ma sana’a ce da ke samar wa mutum kuɗaɗe da zai riƙe kansa da iyalinsa. Tsari ne na zuba jari don samun rayuwa mai inganci a gobe. Waɗannan kalamai na ƙauran Bauchi kuskure ne, da ya kamata gwamnan ya fito bainar jama’a ya janye su. Saboda ba su dace a ji su daga wajen sa ba, a matsayinsa na wanda yake cin ribar ilimin boko, kuma yake ƙoƙari kan bunƙasa shi a jiharsa.

Wannan dambarwa na zuwa ne kwanaki kaɗan da Gwamnan ya ƙaddamar da shirin shigar da makarantun Tsangaya da na Islamiyya cikin tsarin koyar da boko, domin a riƙa koyar da almajiran makarantun allo da ɗaliban madarassa ilimin turanci da lissafi. Kamar yadda yake cikin ƙudirorin Gwamnatin Tarayya, na kawar da yaran da ba sa zuwa makaranta daga titi, da tabbatar da ganin kowanne yaro yana samun ilimin zamani. 

Shamsuddeen Mamuda Ali, wani mai amfani da manhajar Facebook, ya rubuta a ƙasan rubutun Kabiru Lawanti cewa, masu yaɗa wannan ra’ayin da ke nuna sana’a ta fi digiri ko ta fi boko, suna yin haka ne, domin su ƙara kashe zuciyar matasa ’ya’yan talakawa, yayin da ’ya’yansu ke cigaba da samun ilimi a makarantun ƙasashen waje, daga baya su za su karɓi ragamar jagorancin ƙasar. Sun sani sarai idan yaran talakawa suka samu ilimi mai inganci, su nasu yaran ba za su iya gogayya da su ba. Idan ba haka ba, don me ya sa idan yaransu suka kammala karatu, suke shirya bukukuwa don murna, a matsayin wani muhimmin mataki na cigaban rayuwa?

Asusun kula da rayuwar ƙananan yara, da ilimi na Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF) ya sanya sunan Bauchi cikin jihohin da ke da adadin yara masu yawa da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan. Wannan kaɗai ya isa ya janyo cecekuce kan kalaman da Gwamnan ya yi, domin kuwa ana ganin ya yi fami ne kan raunin da ake kokawa a kai.

Hukumar Kula da ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar da ƙiyasin cewa, Jihar Bauchi na daga cikin jihohin Nijeriya mafiya talauci, yayin da kashi saba’in cikin ɗari na al’ummar jihar ke rayuwa cikin ƙangin talauci. Kuma hakan na da nasaba da yawaitar mutane marasa karatu da ƙarancin shiga makaranta. Talauci na samun gindin zama ne a inda jahilci ya yi kakagida.

Wannan na daga cikin abin da ya janyo wani ɓangare na wasu ’yan Nijeriya suke sukar shugabannin Arewa a matsayin waɗanda ke jefa jama’ar su cikin talauci da jahilci, saboda kada su samu wayewar zamani. Ko a baya bayan nan ma an bayyana rashin dacewa da hutun ’yan makaranta da wasu jihohin Arewa suka bayar a lokacin azumin Ramadan, suna masu cewa, hakan na ƙara kashe gwiwar ɗalibai ne daga zuwa makaranta, da rage karsashin su wajen kishin ilimi.

Lallai ya kamata mu riƙa nuna muhimmancin ilimin boko a cikin ayyukan mu da maganganun mu, mu daina kashe gwiwar matasa masu tasowa kan cewar babu abin da ilimin zai tsinana musu. Mun sani muna da ilimin addini wanda shi ma hanya ce ta samun nasara a duniya da lahira. Amma sanin kanmu ne zamani ya zo da komai ilimin ka na addini, idan ba ka yi boko ba, a jahili ake kallon ka. Kuma duk wasu harkoki na rayuwa da cigaba na gwamnati da masu zaman kansu, da ilimin boko ake yin su. Yakamata mu riƙe ilimi kowanne iri ne da muhimmanci sosai, kada mu riƙa nuna wani ɓangare ba shi da muhimmanci, alhalin ko su masu maganganun da ilimin bokon suke taƙama.

Muna ganin abin da aibata boko ya haifarwa ƙasar nan, inda aka salwantar da rayuka masu ɗimbin yawa da dukiyoyi, saboda a lalata duk wani cigaba da ƙasar ta samu ta dalilin ilimin boko. Ayyukan da ƙungiyar ’yan ta’addan Boko Haram suke gudanarwa a ƙasar nan abin takaici ne da Allah wadai, domin kuwa babu wani cigaban da ya kawo mana sai komabaya. Kuma a haka sauran ’yan uwanmu na kudancin ƙasar nan ke yi mana kallon duk tunanin mu akan haramcin boko iri ɗaya ne.

By ukarofi