
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana dakataccen gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara a matsayin ďan gidansa a harkar siyasa duk da rikicin da ke tsakaninsu.
A wata hira da BBC Pidgin ranar Asabar, Wike ya ce ba zai iya faďa da yaronsa ba, yana mai karyata batun da ke cewa sun yi cacar baki a tsakanin su.
Ya ce, faďarsa ba akan Fubara ya ke yi ba, saidai da waɗanda ke angiza gwamnan yi masa tawaye da kokarin sace abinda ba su yi aiki a kai ba.
Ya kuma ce, a yanzu sun ji kunyi saboda an yi galaba akansu a mataki na karshe.
Tun a shekarar 2023 ne rikicin siyasa tsakanin Wike da Fubara ya samo asali, lamarin aka gagara magancewa sakamakon ķamarinsa a tsakanin bangarorin biyu wanda har ya kai ga ya shafi majalisar dokokin jihar.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, Fubara, wanda Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi bayan sanya dokar ta-baci a jihar, ya yi wa Wike aiken sakon bayar da haƙuri a wani mataki na neman sulhu.
