Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kusan shekara ɗaya kenan da kama dagacin tare da wasu matasa bakwai bayan sunyi garkuwa da wata matan aure Zulaihatu Sidi da wani yaron ta inda sai da aka biya su Naira miliyan 20 kafin su sake su.
Harwala yau dagacin na riƙe da muƙamin wakilan Hakimin ‘Yanmaulu a ƙaramar hukumar Ɓaure inda Zulaihatu ke aure.
Matan da ɗan ta sun kwashe kwanaki 10 a hannun ‘yan ta’addan, ta kuma yi zargin anyi mata fyade.
To sai dai ba a daɗe ba wasu fusatattan matasa a garin ‘Yanmaulu suka gudanar da zanga-zanga inda suka zargi masarautar Daura da tsoma baki a maganar a sako dagacin.
To sai dai da yake magana a karon farko Sarkin Daura Umar Farouk Umar ya musanta zargin da matasan suka yiwa masarautar.
Ya ce a tsarin masarautar Daura, Sarki ke da ikon naɗa hakimi sannan shi kuma hakimi ke naɗa dagaci.
Domin haka a cewar Sarkin Daura shi bai ma san wannan dagaci ba kuma “Tuni na bada umurnin tsige bayan samun rahoton aikata ta’addancin.
Sarkin ya nuna rashin jin daɗin sa ga yadda matasan ‘Yanmaulu suka gudanar da zanga-zanga da ya bayyana a matsayin cin mutuncin masarautar Daura.
Ya shawarci mutane su rinƙa zuwa fadar idan suna da wani ƙorafi maimakon su yanke hukunci da kan su.
“Idan kuna da ƙorafi akan duk wani abinda ya dame ku to Ku zo ku same ni komin dare ko rana zan sauraren ku”inji Mai Daura.
A yanzu dai dagacin da sauran mutanen da ake zargi sunan nan ajiye a gidan gyaran hali yayin da ake gudanar da shari’ar su.
