Gwamnan Kaduna ya yi garambawul ga gwamnatinsa da dawo da Ma’aikatar Labarai da El-Rufa’i ya rushe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya dawo da Ma’aikatar Labarai da aka rushe a lokacin gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i a jihar.

Haka kuma, ya sauya wa Kwamishinan Ilimi, Farfesa Mohammed Sani Bello wajen aiki, inda ya naɗa shi matsayin wanda zai jagoranci ma’aikatar.

Gwamnan, ya nada tsohon darakta-janar na Hukumar Makamashi ta Ƙasa kuma tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara akan makamashi, Farfesa Abubakar Sani Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimi.

A sanarwar da Sakataren yaɗa labaran gwamnatin jihar, Ibraheem Musa ya fitar, ya ce gwamnan ya kuma naɗa Gloria Ibrahim a mukamin Kwamishinar Ci-gaban Matasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauye-sauyen da naďin mukaman za su fara aiki nan take.

Uba Sani ya kuma taya su murna gami da kira a gare su da su tabbatar da yin aiki tuķuru don cimma nasarori, wanda yin hakan zai taimaka wajen inganta harkokin ilimi a jihar.

By Babaji