Hukumar Fina-finai ta Ƙasa ta jajenta rasuwar Shugaban MOPPAN, Umar Maikuďi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kula da Fina-finan Nijeriya (NFC), ta bayyana alhininta bisa rashin Alhaji Umar Maikuďi, wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan harkar fina-finai a Nijeriya.

A sanarwar da ta fitar a Jos, hukumar ta koka game da rashin shugaban na ķungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, duba da gudumawarsa ga ci-gaban harkar fim a Nijeriya musamman ga masana’antar Kannywood.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan hulďa da jama’ar hukumar, Brian Etuk, Darakta-Manaja na NFC kuma babban jarumin Kannywood, Dakta Ali Nuhu ya bayyana kaďuwarsa game da rashin, wanda ya ce ya haifar da babban giɓi musamman wajen harkokin jagoranci.

Ya kuma ce, marigayin ya bar giɓi ga iyalansa da mambobin MOPPAN duba da ƙoƙarinsa wajen samar da damanmaki ga masu shirya fina-finai a Nijeriya da ma ƙasashen waje.

Dakta Nuhu ya kuma miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalansa da ƴan uwa da abokan arziƙi, yana mai masa fatan samun rahamar Allah SWT.

By Babaji