Majalisar Wakilan Nijeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ‘yan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Majalisar Wakilan Nijeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ceto ‘yan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya sakamakon sabbin sauye-sauyen dokokin ayyukan ƙwadogo da hukumomin Saudiyya suka bijiro da su.

ɗan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Shehu ne ya gabatar da ƙudurin a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

A baya-bayan nan ne dai hukumomin Saudiyya suka bijiro da wasu sauye-sauye kan dokokin da suka shafi ayyukan baƙi a ƙasar, ciki har da daina sabunta takardun izinin aiki a ƙasar ga wasu mutanen.

Hon. Muhammad Shehu ya ce sauye-sauyen sun tilasta wa wasu ‘yan Nijeriya da dame da ke zaune a Saudiyya rasa ayyukansu, yayin da wasu ke fuskantar tsadar kuɗin sabunta takardunsu.

“ɓangaren zartarwa ta hannun ma’aikatar kula da harkokin ƙasashen waje ba su tuntuɓi hukumomin Saudiyya kan wannan batu ba da nufin samar wa ‘yanƙasarmu sauƙi, ko yin wani shiri na kwaso mutanen domin maido su Nijeriya ba,” kamar yadda ya bayyana.

Haka kuma ɗan majalaisar ya yi kira ga hukumomin Saudiyya ta sassauta tare da yin la’akari ga mutanen da ke da sha’awar komawa gida.

By ukarofi