
Daga BELLO A. BABAJI
Mutane uku sun rasu yayin da aka garzaya da ɗaya zuwa asibiti a lokacin da suka ci wani abinci mai ɗauke da guba a garin Magama dake Ƙaramar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
Ƙwararre mai sharhi kan daƙile ayyukan ta’addanci, Zagazola Makama ya faɗi hakan a wani sako ta kafar X, ranar Alhamis.
Ya ce, mamatan sune Hussaina Ayuba, Ahmed Ayuba, and Nana Ayuba.
An garzaya da su Babban Asibitin Jibiya ne a lokacin da suka ci taliya, inda suak rasu jim-kaďan bayan hakan.
Ya kuma ce, Hafsat Ayuba mai shekaru 12 tana karɓar magani a asibitin.
Haka kuma, an kama wanda ake zargi – wata mai suna Fatima Abdulkadir, wadda ita ta girka abincin tare da wasu mutane biyu da hannu a aikata laifin.
