Matasan Arewa sun buƙaci a duƙufa yi wa ƙasa addu’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Ci gaban Matasan Arewa (AYAF) ta ce akwai buƙatar ’yan Nijeriya su koma ga Allah ta hanyar yi wa ƙasar addu’o’i domin samun waraka daga matsalolin da take fuskanta.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwar bayan taronta a Abuja a ƙarƙashin shugabancin Mukhtar Sagir Dambatta, inda ta buƙaci ’yan Nujeriya su dage da addu’a domin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta, musamman rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.

Kungiyar ta ce, matsalolin da ƙasar ke fuskanta za su faskara matuƙar ba a koma ga Allah ba domin neman taimakonsa da kariyarsa.

ƙungiyar ta kuma yi kira ga ’yan ƙasar baki ɗaya da su bayar da gudunmuwarsu wajen ilimantarwa, “domin da ilimi da aikin taimakon kai da kai da kuma haɗin kai ne za a iya ganowa tare da magance dukkan matsalolin da al’umma suke fuskanta tun kafin su girmama,” inji sanarwar.

By ukarofi