Zuwa ga Majalisar Dattawan Nijeriya

Spread the love



A game da ayyukan ta’addanci da ƙungiyar Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da yi a yankin Borno a yanzu, tura ƙarin sojoji ba shi ne mafita ba, ba kuma shi ne abin da ya dace ayi ba.

Duk yawan mayaƙan Boko Haram da duk wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da ke jihar Borno, na tabbata sojojin Nijeriya da ke jihar Borno sun isa su kakkaɓe duk wata ƙungiyar ta’addanci, matuƙar za a ba su damar yin hakan.

Muna da haziƙai kuma zaƙaƙuran jami’an tsaron soji a Nijeriya, waɗanda suka ƙware wajen iya aiki. Amma babbar matsalar ita ce, manyan jagororin ƙasar nan da suka haɗar da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da manya-manyan jami’an gwamnati da ma wasu daga cikin manyan jami’an tsaron, sun kasance ‘yan rashawa da karɓar cin hanci da kashe mu raba.

To irin waɗannan gurɓataccin manyan mutanen su ne suke kawo koma-baya a harkar tsaro. Na tabbatar a yadda sojojin ƙasar nan suke da ƙoƙari da juriya a wajen yaƙi da tunkarar abokan gaba, babu wata ƙungiyar ta’addanci da zata gagari sojojin Nijeriya.

Saboda haka, idan har ana so a kawo ƙarshen duk wata ƙungiyar ta’addanci ba wai iya Boko Haram da wata ISWAP ba, to ya kamata a ƙyale sojoji da sauran jami’an tsaro suyi aikinsu bil-haƙƙi da gaskiya.

Sojojin Nijeriya ba ragwaye ba ne, amma saboda son zuciya an saka siyasa da kwaɗayi a cikin dukkan al’amurran Nijeriya, kullum ƙasar tana komawa baya maimakon taci gaba, wanda hakan na faruwa ne saboda rashin adalci, kishin al’umma da kishin ƙasa da rashin jin tsoron Allah da manyan ƙasa da jagororin al’umma suka rasa a zukatansu.

A matsayina na marubuci, wallahi na aalubalanci duk wanda ya ce sojojin Nijeriya ba za su iya kawar da duk wata ƙungiyar ‘yan ta’adda ba.

‘Yan Nijeriya kuje ku binciki tarihin Marigayi Janar Hassan Usman Katsina, Janar Murtala Ramat, da Janar Abacha da Marigayi Lt. Janar Ibrahim Attahiru, kuma Janar Ali Keffi da ke raye a yanzu, wanda a cikin wannan watan ya rubuta wa shugaban Nijeriya Tinubu wasiƙa a kan Boko Haram. Me ya sa aka kashe Ibrahim Attahiru? Me yasa aka yi wa Janar Ali-Keffi ritaya saboda ya kama kwamandan Boko Haram?

Tun daga ƙungiyoyin dake rajin kare haƙƙin ɗan Adam, irin su AMNASTE INTERNATIONAL da ire-iren su dake yin iface-iface a kan kare haƙƙoƙi da ‘yancin ‘yan Adam, duk ɓaɓatun iska kawai suke yi ba da gaske suke yi ba. Idan kuma da gaske ne zuwa yanzu a faɗa mana haƙƙoƙin rayukan jami’an tsaron mu na Nijeriya da aka kashe a bisa zalunci nawa suka karɓo a matsayinsu na ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam?

Dole ne mu faɗa wa kanmu da manyan ƙasarmu gaskiya a kan yadda suka bari ta’addanci ya mamaye mana ƙasa. Shin son zuciya ne ko kuma kwaɗayin tara abin duniya? Kowacce ƙasa ƙoƙarinta kare martabar ƙasarta da kuma ganin ƙasar ta haɓɓaka ta kowanne fanni, amma jagororin al’umma a Nijeriya ba ta wannan suke yi ba. Abin da suka fi mayar da hankali bai wuce gasar gina manyan gidaje da hawa manya-manyan motocin alfarma ba. Sai kuma idan ka zamo mai faɗa musu gaskiya da gwamnatinsa, shi kenan ka zamo ɗan adawa da kullum a cikin barazana da rashin kwanciyar hankali ka ke, abinda ake so kawai ka koma gefe kana ji kana gani ana aikata ba daidai ba ka zuba ido kaja bakinka kayi shiru, zaka yi hakan ne idan ba ka yarda ka shiga cikinsu ayi wadaƙa da kai ba.

Haka zalika, idan kuma zaka shiga cikinsu, to a nan ma sai ka ja bakinka kayi shiru, ka rantse idonka, duk abin da ake yi ka zama makaho ka zama kurma ba kaji ba ka gani, duk ɓarnar da za ayi ta cin hanci da rashawa kar ka tsoma baki.

Haka nan dole zaka zamo mai kare muradunsu a fili da ɓoye, a kafafen watsa labarai ko a cikin jaridu da mujallu da gidajen Talabijin, sai ka zamo mai kare su da muradunsu. To idan kayi haka, shi ne zaka zauna lafiya kuma babu wanda zai taɓa ka. Kayi ƙarya su baka kuɗi, ka zagi wannan da wancan a siya maka mota a baka kuɗi, kayi rantsuwa a kan ƙarya wajen kare su su ƙara jawo ka jikinsu.

To amma kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda yake da abin da zai ci, amma ya mayar da roƙon mutane ta hanyar fadanci da babaɗanci don a bashi kuɗi, kuma yayi amfani da kuɗin wajen cin abinci da sanya sutura, to ya sani cewa garwashin wutar Jahannama yake ci.” Haka nan Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce; “A duk lokacin da kaga ana aikata ɓarna to kayi ƙoƙari ka hana idan zaka iya, idan ba zaka iya hanawa a hanu ba to ka ƙyamaci abun, ko ka tashi ka bar wajen.”

Haka zalika, Manzon Allah (S.A.W) ya ce; “Duk wani shugaba da ya jogaranci al’umma, to za a zo dashi a gaban Allah ranar Alƙiyama ɗaure cikin sasari (sarƙa), adalcinsa ga al’ummar da ya mulka shi zai kwance shi.”

A matsayinka na shugaban ƙasa, dole ne ka damu da talakawan ka, ka kuma ji tausayinsu tare da ƙoƙarin sauke nauyin haƙƙinsu da ya rataya a kanka. A matsayinka na gwamna, dole ka kula da mutanen jiharka da kake shugabanta, ka sauke nauyin da Allah ya ɗora maka. Sai kafin damuwa da al’umma fiye da kanka da iyalinka sannan za ka zamo shugaba adali. A matsayinka na ɗan majalisa, dole ka kula da jama’ar da kake wakilta domin kai ne wakilinsu, kuma wajibi ne ka riƙa zama dasu kana jin damuwarsu sannan ka isar da koken su inda za a share musu hawaye.

Don haka, batun tura jami’an tsaro Maiduguri ba shi ne mafi alaƙa ba, abin da kawai za a yi shi ne, a bar sojoji da sauran jami’an tsaro suyi aikinsu tsakani da Allah, a ƙara musu makamai da duk wani abu da ya dace. Idan aka yi haka, to ina tabbatar da cewa a irin ƙwarewa da juriya gami da haƙuri da sojojin ƙasarmu suke dashi, a ɗan ƙanƙanin lokaci za su kawo ƙarshen duk wata ƙungiyar ta’addanci a ƙasar nan. Amma a wasu lokutan sai kwamandan soji ya jagoranci rundunarsa sun tunkari maɓoyar ‘yan ta’adda, kawai sai a yi masa waya daga sama a ce ya biyo, shi kuma dole ya juyo saboda na gaba da shi ne suka ba shi umarni.

Akwai sauran bayanai a gaba zan yi su.

Nafiu Salisu. Marubuci/Mana zargi. [email protected]@yahoo.com. 08038981211-09056507471. 

By ukarofi