Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Hukumar hana cin hanci da rashawa ta Jihar jigawa ta cafke shugaban bankin tsimi da lamuni na Jihar jigawa ta kuma gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin samun sa da almundahana.
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa itace ta shigar da ƙarar shugaban bankin tsimi da bada lamuni na jihar Jigawa a gaban kotun majastare ta biyu da ke zamanta a Dutse bayan ta kama shi a ranar Alhamis da ta gabata bisa zargin al’mundahana.
Hukumar tace ta kai batun kotu ne domin cigaba da bincike da kuma yanke hukunci kan zarge-zargen da a ke masa.
Lauyar hukumar mai ikirarin hana cin hanci da rashawa ta Jihar jigawa wato JSPCACC Barista A’isha Ɗangote ce ta shigar da ƙarar a madadin hukumar tare da gabatar da ƙorafe-ƙorafen da hukumar take tuhumar sa da su a gaban kotun.
Nan take kuma wanda ake zargi ya musanta zargin da hukumar take masa ta bakin lauyan sa Barista Husaini Magama tare da neman kotun ta bada belin wanda yake karewa.
Alƙalin kotun mai shari’a Abdullahi Ibrahim Aliyu ya tuntuɓi lauyar hukumar da take ƙara kan wannan buƙata kuma ta amince inda alƙalin kotun ya bada belin wanda ake zargin kan sharuɗa guda uku da suka haɗa da bada kuɗi naira Miliyan 20,000,000, kawo masu tsaya masa guda biyu ɗan majalisar jaha da hakimin ƙasar sa dakuma bada duk wasu takardun sa na tafiye-tafiye.
Tuni sai alƙalin kotun mai shari’a Abdullahi Ibrahim Aliyu ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 03/06/ 2025.
