
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ce Gwamnatin Tarayya ta haramta wa ƙasashe takwas shigowa Nijeriya a makon da ya gabata sakamakon samun su da bizozin da suka tashi daga aiki.
Dakta Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a yayin hira da tashar TVC a daren ranar Lahad inda ya ce ma’aikatar ba za ta sake amincewa da shigowar ƴan ƙasashen waje ba ba tare da cika ƙa’ida ba.
Ya kuma ce, ya gana da wakilan kamfanonin jiragen sama a ranar Juma’a, inda ya tattauna da su akan sababbin matakai da aka bijiro da su game da shiga ko fita daga Nijeriya, yana mai cewa ba za a sake barin wani ya shigo ƙasar ba tare da biza ba.
Kazalika, Ministan ya gargaɗi kamfanoni game da bijire wa dokar, inda ya ce duk kamfanin da ya shigo da fasinjoji ba tare da sahihan bizozi ba, to za a hukunta shi bisa yadda doka ta tanada.
Tunji-Ojo ya kuma jaddada ƙoƙarin gwamnati na kare ɓangaren tsaro a ƙasa da kiyaye dokokin shige da fice.
