Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Ko’ina ya karade da wata sanarwa da aka alakanta da Kwankwaso cewa ba zai shiga APC ba, sai kuma kwatsam ga sanarwa ta shafinsa na Twitter (ɗ) ya na karyatawa. Mutane da dama sun ji dadin sanarwar ta farko yadda cikin kankanin lokaci ta zama ɓiral. Amma sai ya kashewa mutane gwiwa da sanarwarsa ta baya.
Wato ga duk wanda ya bibiyi siyasar Kwankwaso tsawon shekaru sama da ashirin tun dawowar wannan siyasa, zai fahimci cewa mutum ne wanda hausawa ke kira da “Alu Ja”, shi Alu ja, ba wanda ya ke bi sai dai a bi shi. Duk irin gudunmuwa da Abubakar Rimi, Musa Gwadabe da Senator Hamisu Musu su ka ba shi a matsayin masu gidansa, daga baya duk ya fandare musu, saboda bai son ace ya yi, sai dai shi ya ce a yi.
A lokacin mulkin dawo-dawo, wato zangonsa na biyu (2011-2015) ya bijiro da ayyuka da ba’a taba ganin wani Gwamna a tarihi ya kaddamar da ayyuka a lokaci guda irinsa ba. Kama daga Ilimi da ayyukan more rayuwa a kusan kowane fanni na rayuwa. Abinda ya sa ni kaina na rubuta masa littafi da sahalewar gwamnatinsa me suna “Manyan Ayyukan da Kwankwaso ya Aiwatar”. To daga baya sai na gane cewa ashe duk wadannan ayyuka, ya bijiro da su ne da burin su taimaka masa samun takarar shugaban kasa a 2015. Kuma hakika sun taimaka domin sai da ya buge Atiku ya zama na biyu a wadanda suka tsaya takarar.
Maimakon a wannan lokaci ya kwashi duk kudade da kayan kamfen dinsa ya narkar da su a kamfen din Buhari, sai ya noke. Shi kuma Dan Daura kun san shi da riko, don haka da aka kafa gwamnatin APC ya yi watsi da Kwankwaso har ya gama mulkinsa.
Da aka zo zaben 2023, sai shugaban darikar Kwankwasiyyar ya sake nokewa, ya ki goyon bayan Tinubu ballantana Atiku. Hali zanen dutse, don haka Kwankwaso yayi tsayuwar Alu Ja, ya ja daga shi kadai. Ya sami kuri’a sama da miliyan daya, wadda ba ta da tasirin karkata zaben hagu ko dama, wato ko ya ba Tinubu ko ya ba Atiku, wannan kuri’a miliyan daya ba za ta canza akalar zaben ba, domin ba zata sa Atiku ya ci ba, kuma rashinta ba zai sa Tinubu ya fadi ba. Wato fancalen ma ba ta kai ba kenan. Don haka kun ga kuri’arsa bata da tasiri a zaben kasa (national elections).
To a yanzu da ake dosar zaben 2027, da alamu dai mai hali baya barin halinsa, kuma bayan rade-radin zai shiga ko ba zai shiga APC ba, Kwankwaso ya ki fitar da tarbiyar matsaya. Alamun cewa dai bashi ga tsuntsu, ba shi ga tarko har yanzu.
Jan hankali ga Kwankwaso da magoya bayansa shine, su sani cewa idan za’a shekara miliyan a irin wannan tafiya da Kwankwaso ke yi, to wallahi har abada ba zai yi tasiri a siyasar sama ba (National politics), haka nan zai kare a local champion na yan Kwankwasiyya kawai a Kano. Ita siyasa dole sai da hadaka, da sadaukar da bukata domin cimma wani buri.
Malam Ali Sadiƙ manazarcin harkokin yau da kullum ne a Kano. Za a iya samun sa a +2348039702951
