Daga CHIROMA AMINU ASID
Gonorrhea wata cuta ce da ƙwayar halittar ‘bacteria’ da ake kira ‘Bacterium Nieserria’ take kawowa, wacce ta kan iya shafar maza ko mata.
Yawanci wannan cutar ta kan shafi ɓangaren mafitsara ne (urethra), dubura (rectum) ko maƙogaro (throat), inda ga mata ma wani lokacin ta kan shafi mahaifarsu (cerɓiɗ).
Wannan cutar ta kan yaɗu ne ta dalilin saduwa da mai matsalar ko ta jaririn da mahaifiyarsa take fama da matsalar, sannan wasu lokutan ta na shafar idanu ne. Sau da dama wasu lokutan Gonorrhea ba ta bayyana alamu.
Alamomin cutar sanyi (Gonorrhea):
Kamar yadda na faɗa ita wannan cuta ba ta cika nuna alamu ba ko da kuwa ka na da ita sai dai idan ta nuna alamu yawanci kuma ta kan iya shafar na wani sahen a jikinka, musamman ma ɓangaren al’aurarka (genital track).
Alamun wannan cuta ga maza sun haɗar da;
1.Jin zafi yayin fitsari.
2.Ganin farin ruwa tsinkakke, kamar nono haka ya fito a gaba bayan gama fitsari.
3.Jin zafi ko kumburin testicle guda ɗaya.
Alamominsa ga mata kuma shi ma sun haɗar da;
1. Fitar da farin ruwa sossai a gaba.
2. Jin zafi yayin fitsari.
3. Zubar jini kafin lokacin al’ada ko bayan mu’amalar aure.
4. Ciwon ciki.
5. Ciwon baya da sauransu.
Gonorrhea, idan ya kasance ta shafi wani sashen saɓanin al’aura (genital track) shi ma ya danganta da ina ta kama. Misali;
Rectum: Al’amomin da za a gane sun haɗar da ƙaiƙayin gaba, fitar farin ruwa daga dubura da sauransu.
Ido: Idan ya kasance ta taɓa idonka za ka riƙa jin zafi a ido, jin raɗaɗi, idan ka shigo rana, fitar farin ruwa a ido ɗaya ko duka da sauransu.
Sannan ta na iya shafar maƙogaro, gaɓoɓi da sauransu.
Insha Allah zuwa rubutu na gaba za mu yi jawabi a kan masu haɗarin kamuwa da matsalar, hanyoyin kare kai ko samun sauƙin matsalar, sannan da abubuwan da su kan iya faruwa idan aka yi burus da matsalar.
