Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin neman wajabta zaɓe bayan al’umma ta koka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya janye ƙudirin da ke neman a wajabta wa al’umma kaɗa kuri’a a lokutan zaɓe.

Kakakin majalisar da ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Bassa/Jos (Filato), Daniel Ago ne suka ɗauki nauyin ƙudirin.

Saidai, a yayin zaman majalisar na ranar Litinin, bayan samun ƙorafe-ƙorafen al’umma game da kaďuwa da suka nuna a kai, majalisar ta yanke hukuncin janye ƙudirin.

A sanarwar da mai taimaka wa Kakakin akan harkar labarai, Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Abbas ya ce an gabatar da ƙudirin ne da nufin faɗaɗa adadin masu zaɓe duba da ƙarancinsa da ake samu a yayin zaɓuka, lamarin da ke haifar da tsaiko a lamuran zaɓukan Nijeriya.

Ya sanar da cewa, bisa la’akari da tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki gami da shawarwari da suka samu, ya yanke shawarar janye ƙudirin, wanda ke naman a yi kwaskwarima ga dokar zaɓe ta 2022.

Ya ƙara da cewa, samar da doka abu ne da kai-tsaye ya shafi waɗanda ake yi wa aiki, inda duk lokacin da aka yi yunƙurin samar da sauyi, sai an yi la’akari da ƴanci da maslahar al’umma kafin aiwatarwa.

By Babaji