
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Yanayi (NiMET) ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohi guda 14 a Nijeriya har na tsawon kwana uku.
Jihohin sune Bayelsa, Ribas, Delta, Ondo, Edo, Akwa-Ibom, Kuros-Riba, Imo, Abia, Abuja, Kaduna, Nasarawa, Kogi da Neja.
Ranakun sune daga Laraba, 28 zuwa Juma’a, 30 ga watan Mayu.
Ta kuma ce, akwai yiwuwar a samu iska a yayin ruwan saman gami da ambaliya a wasu yankunan.
Haka kuma ta shawarci jama’a da kada su yi zirga-zirga a yankunan da ruwa ke taruwa, waɗanda akwai yiwuwar su haddasa ambaliya ko cinkoson ababen hawa.
