Hukumar samar da ruwa ta jihar Bauchi ta samu sabbin kayan aiki don magance ƙarancin ruwan sha

Spread the love

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi

Ganin yadda ake fama da matsalar ƙarancin ruwan sha a cikin garin Bauchi da kewaye da kuma wasu ƙananan hukumomi na jihar Bauchi, Hukumar samar da ruwa ta jihar ta bayyana ƙoƙarin gwamnatin jihar Bauchi na samar da sabbin na’urorin samar da hasken lantarki domin tallafawa hasken lantarki na ƙasa don a magance matsalar da ke haifar da ƙarancin ruwa a unguwanni da garuruwa.

Injiniya Aminu Aliyu Gital, babban Manajan hukumar samar da ruwa ta jihar Bauchi shi ne ya bayyana haka cikin hirarsa da manema labarai a ofishinsa da ke hukumar samar da ruwan a Bauchi.

Yadda cikin jawabinsa ya gode wa Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi saboda samar da na’urorin transfoma da sabbin injina don samar da hasken lantarki a dukkan tashoshin samar da ruwa da ke cikin garin Bauchi da kewaye.

Ya ce an yi duk ayyukan da suka dace yadda a halin yanzu dukkan wuraren da suke da bututun tura ruwa za su ci gaba da samun ruwa sosai. Wuraren da ba su da layin ruwa kuma su ƙara haƙuri har zuwa lokacin da za a ci gaba da faɗaɗa aikin kamar yadda aka yi shekara biyar da suka wuce, saboda a kullum garin Bauchi yana ƙara samun sabbin unguwanni saboda shigowa da ake yi daga wasu garuruwa masu fama da rashin zaman lafiya.

Injiniya Aminu Aliyu Gital ya ce shekaru biyar kenan aka yi aikin faɗaɗa hanyoyin adana ruwan da kuma dasa sabbin bututai da sauran kayan aiki irin na zamani.

Don haka ya buƙaci ma’aikatan hukumar su inganta ayyukansu ta hanyar amfani da kayan kariya da suka dace don kiyaye aikin su da rayukansu a bakin aiki. 

Don haka Aminu Aliyu Gital ya bayyana takaici game da hatsarin da wasu ma’aikatan hukumar huɗu suka shiga a kwanakin baya har suka rasa rayuwarsu a yadda aka dasa injinan tace ruwan. Don haka ya bayyana cewa hukumar ta ɗauki duk wani mataimakin da ya dace don ganin hakan bai sake faruwa ba.

Daga ƙarshe ya roƙi jama’a su riƙa lura da kayan da aka samar a wuraren su don ganin ɓatagari basu lalata ko sun sace ba. Sai mutane sun taimaki gwamnati kafin ta samu zarafin inganta rayuwar jama’ar ta.

By ukarofi