Raɗɗa ya gargaɗi ‘yan APC a Katsina su guji cin mutuncin mambobin jam’iyyar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina yayi wannan gargaɗi a garin Musawa lokacin da ya je ƙaddamar da aikin hanya a ƙaramar hukumar ta Musawa.

Yace dole su rinƙa mutunta juna ,kuma su guji duk abinda zai kawo rarrabuwar Kawuna da faɗa ce faɗa ce tare da kawo rabuwar Kawuna a tsakanin ya’yan jam’iyar.

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan a kwanakin baya aka sami rashin jituwa a tsakanin mataimakin shugaban jam’iyar APC na jihar Bala Abu Musawa da ɗan majalisar tarayya Hon Abdullahi Aliyu Dujiman Katsina waɗanda dukkan su ƴan ƙaramar hukumar Musawa ne.

To sai daga baya sun sasanta a tsakanin su bayan da gwamna Dikko Raɗɗa ya shiga tsakani.

Gwamnan ya ƙaddamar da aikin hanyar mai tsawon kilomita 19 da ta tashi da marabar Musawa ta je kirkiran zuwa Gingin ta isa Gabannin inda tayi iyaka da ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Malam Dikko Radda ya bayyana cewa hanyar idan an kammala za ta taimaka wa manoma wajen haɓaka arzikin yankin.

Yayi kira ga al’ummar yankin da su cigaba da yiwa gwamnati addu’a domin samun damar cigaba da ayyukan alheri a yankin da jihar Katsina baki ɗaya.

By ukarofi