Hukumomin Saudiyya sun gabatar da sabbin matakan kariya bayan matakin zafi ya haura digiri 50

Spread the love
Muslim pilgrims join one of the hajj rituals on Mount Arafat near Mecca early on Sunday.

Daga BELLO A. BABAJI

Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya fitar da sababbin matakan kariya ga masu aikin hajji, inda ta yi kira a gare su da su kiyaye halin da ake ciki duba da tsananin zafi da ake fama da shi.

Hakan na zuwa ne a yayin da matakin zafi a ƙasar ya haura digiri 50 domin tabbatar da kammala aikin hajjin cikin lumana.

Akan haka ne hukumomin suka nemi mahajjatan da kada su fito daga masaukinsu daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, lamarin da ya shafi hatta ziyara zuwa dutsen ‘Jabal Noor’ a lokutan tsananin zafi.

Ma’aikatar ta kuma ce, zirga-zirga daga Arafa zuwa Muzɗalifa, za a yi su ne kaɗai ta motocin da hukumomi suka ware domin kauce wa agajin gaggawa a sanadiyyar zafi.

Haka kuma mahajjatan za su yi Udhiya da Hadaya ne ta hanyoyin da aka amince su, inda nan ba da jimawa ba za a fitar da bayanai akan haka.

An kuma kirayi jami’an aikin hajji da ƴan jarida da su isar da saƙon sharuɗɗan ga mahajjata domin tabbatar da kiyaye su da bada kariya a gare su a yayin gudanar da harkokin ibadar.

By Babaji