Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ɓangaren haƙar ma’adinai na Nijeriya ya samu gagarumar nasara, wanda Ministan Raya Ma’adinai, Dr. Dele Alake, ya bayyana a matsayin “ci gaba mafi girma da aka taɓa samu a tarihin Nijeriya” a wannan fanni.
A cewar Ministan, kuɗaɗen shiga daga harkar ma’adinai sun ƙaru daga Naira Biliyan 6 a baya zuwa Naira Biliyan 38 a shekarar 2024, hakan ya kai ninki shida cikin shekara guda. Wannan ci gaban ya biyo bayan sabbin dokoki da aka kafa, waɗanda suka haɗa da tsauraran sharuɗɗan bayar da lasisi da kuma wajabcin sarrafa ma’adinai a cikin gida kafin a fitar da su zuwa ƙasashen waje.
Sabbin matakan sun janyo hannun jari daga ƙasashen waje da ya kai fiye da dala miliyan 800, inda manyan ƙasashen duniya suka fara nuna sha’awa da niyyar saka jari a fannin ma’adinan da duniya ke matuƙar buƙata.
Daga cikin manyan ayyukan da Ma’aikatar Raya Ma’adinai ke aiwatarwa sun haɗa da; Masana’antar lithium mai darajar dala miliyan 600 a kan iyakar Kaduna da Jihar Neja, Masana’antar tace ma’adinai mai darajar dala miliyan 200 a Abuja, wacce ke daf da kammalawa, da kuma masana’antu biyu da za a gina a Jihar Nasarawa a zangon uku na shekarar 2025.
Duk da cewa an saki kashi 18 kacal daga cikin kasafin kuɗin ma’aikatar wanda ya kai naira biliyan 29, an samu nasarori masu girman gaske. A zangon farko na shekarar 2025, Hukumar Rijistar Ma’adinai (MCO) da Sashen Binciken Ma’adinai sun tara kuɗaɗe har naira biliyan 6.9 da naira biliyan 7, wanda ya wuce yawan da ake samu a baya.
A wani mataki na tabbatar da daidaito, Ministan ya ce an kama sama da mutum 300 da ke haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da kafa gamayyar haƙar ma’adinai fiye da 250 domin ƙarfafa harkar. Haka kuma, Nijeriya ta samu matsayin jagorantar ƙungiyar Dabarar Ma’adinai ta Nahiyar Afirka (Africa’s Mineral Strategy Group).
Gwamnatin Tarayya kuma ta ƙaddamar da kasafin kuɗin Naira Tiriliyan 1 wanda zai taimaka wajen janyo ƙarin jarin ƙasashen waje.
Al’umma da masana tattalin arziki sun bayyana matakin gwamnatin Tinubu a matsayin sauyi mai ma’ana da zai iya canza fasalin tattalin arzikin Nijeriya gaba ɗaya, musamman ma a fannin da aka jima ana watsi da shi.
Wannan ci gaba wata alama ce ta yadda shugabanci mai hangen nesa da tsare-tsaren da suka dace za su iya farfado da sassan tattalin arzikin ƙasa da ke da tasiri wajen samar da aikin yi, ƙara kuɗaɗen shiga da tabbatar da ci gaban ƙasa mai ɗorewa.
