Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Jihar Bauchi BASIEC, ta gudanar da zaɓen cike gurbi a ƙaramar Hukumar Shira a ranar Asabar 24 ga Mayu, 2025.
Tun a ranar Juma’a 23 ga watan Mayu hukumar ta BASIEC ta raba muhimman kayayyakin gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar Shira don cike gurbin shugaban ƙaramar hukumar wanda kansiloli suka tsige shi tare da mataimakinsa a kwanakin baya.
Shugaban hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta a jihar Bauchi BASIEC, Alhaji Ahmed Makama shine ya jagoranci raba kayan zaɓen ranar Juma’a a harabar ofishin hukumar a Bauchi, kuma ba tare da ɓata lokaci ba aka kwashi kayan da suka haɗa da akwatunan jefa ƙuri’a da takardun zaɓe da sauran muhimman kayan aikin zaɓen zuwa ƙaramar hukumar ta Shira.
A ranar Asabar da safe mutane suka fita rumfunan zaɓe guda 249 yadda jami’an zaɓen suka gudanar da aikin zuwa yammaci bayan an kammala, jagora mai tattara zaɓen Malam Kabiru Abba ya kawo sakamakon zuwa ofishin hukumar da ke Bauchi.
Shugaban hukumar zaɓen Alhaji Ahmed Makama ya bayyana jam’iyyun siyasa uku ne suka shiga zaɓen.
Cikin su akwai jam’iyyar ADC wacce Yakubu Ayuba ya tsaya takara tare da mataimakin sa Sulaiman Ibrahim Datti, yadda suka samu guri’u 241.
Sai kuma jam’iyyar YPP wacce Shafi’u Haladu ya tsaya takara da mataimakinsa Bello Garba kuma sun samu guri’u 293.
Sai Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Bauchi wacce Babangida Ishak Abdullahi Maliya, ya tsaya takara tare da mataimakinsa Ali A. Adamu kuma sun samu nasara da ƙuri’u dubu 47,361 yadda suka lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.
Jam’iyyar APC babbar mai adawa a jihar Bauchi bata samu shiga zaɓen ba. Kuma tun farko ta bayyana rashin gamsuwa da yadda aka shirya gudanar da zaɓen, don haka ta rubuta takardar janyewa daga shiga zaɓen zuwa ga hukumar ta BASIEC.
Wata majiya mai tushe ta bayyana mana cewa bayan haka kuma sun garzaya kotu yadda suka buƙaci a dakatar da gudanar da zaɓen har sai an yi gyare-gyaren da za su gamsu. Majiyar ta bayyana mana tuni kotun ta sa watan Yuni don fara sauraron ƙarar.
Dukkan ƙoƙarin da muka yi don jin ta bakin shugabannin jam’iyyar ta APC ya ci tura. Amma a duk lokacin da muka ji daga gare su za mu sanar da jama’a.
Bayan kammala sanar da sakamakon zaɓen a harabar hukumar ta BASIEC a Bauchi a yammacin Asabar a gaban kwamishinonin hukumar da sauran ‘yan siyasa da ‘yan gudu, shugaban hukumar ta BASIEC Alhaji Ahmed Makama ya bayar da takardun shaidar cin zaben wa Alhaji Babangida Ishak Maliya da mataimakin sa Ali A. Adamu.
Kuma ya bayyana cewa an yi zaɓen lafiya an gama lafiya, kuma mutane sun fito sosai fiye da sauran zaɓukan gama gari da suka gudana kwanakin baya a dukkan ƙananan hukumomi 20 na jihar Bauchi.
Don haka Ahmed Makama ya yi fatar Alheri da neman Allah ya ba sabbin shugabannin ƙaramar hukumar ta Shira iko da damar gudanar da jagoranci bisa bin doka da adalci da nuna gaskiya ga mutanen da suka zaɓe su cikin nasara.
.
