
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne Shugaba Donald Trump na Amurka ya amince da hana ƴan ƙasashe guda 12 zuwa ƙasar.
Ƙasashen sune Afghanistan, Myanmar, Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libiya, Somaliya, Sudan, da Yemen.
Dokar, ta nuna cewa mutane daga ƙasashen da aka lissafo ba za a bari su shiga ƙasar ba bisa kowane irin dalili.
A ranar 9 wata Yuni, 2025 ne dokar za ta fara aiki, wanda zai yi daidai da ƙarfe 5:01 na safe a Nijeriya.
Hakan wani ɓangare ne na ƙarfafa dokokin shige da fice na zangon mulkinsa na biyu.
Haka kuma, Trump ya taƙaice wa ƴan ƙasashen Burundi, Cuba, Laos, Sierra Leone, Togo, Turkmenistan da Venezuela tafiye-tafiye a ƙasar, lamarin da zai sa a tsaurara matakan bincike akansu da taƙaice ba su biza.
Trump ya ce, ya yi hakan ne da nufin dakatar da mutanen da ka iya zama barazana ga ƙasar, yana mai cewa wasu daga cikin ƙasashen suna da ƙungiyoyin ƴan ta’adda masu ƙarfi da ke ayyukansu a iyakokinsu.
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa, wasu daga cikin ƙasashen sun gaza tanadar cikakkun bayanai akan ƴaƴansu, wanda ta haka ne za a iya duba tarihinsu musamman a game da manyan laifuka a yayin da suke neman bizar shiga Amurka.
Trump har’ilayau ya ce, akwai adadi mai yawa na ƴaƴan ƙasashen, waɗanda suka zauna a Amurka na tsawon sama da wa’adin bizarsu.
Wannan ba shi ne karon farko da Trump ke yin irin haka ba, inda a wa’adinsa na farko a shekarar 2018 ya haramta wa ƙasashe bakwai shiga Amurka, lamarin da ya kai ga tafka shari’a a tsakanin gwamnatinsa da waɗanda abin ya shafa.
Daga bisani a shekarar 2021, tsohon shugaban ƙasar Joe Biden ya soke haramcin, matakin da ya bayyana a matsayin rashin adalci.
