Abin da ya haddasa ambaliyar Neja – Gwamnati

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ce, sauyin yanayi da rashin bin ƙa’idar gine-gine da rashin gyara magunan ruwa ne suka haddasa mummunar ambaliyar da ta auku a garin Mokwa na jihar Neja.

Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli na Nijeriya, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka a Abuja, yayin da yake bayani kan ambaliyar da ra auka wa garin Mokwa na jihar Neja.

Ministan ya ce, ba ɓallewar madatsun ruwa na Kainji da Jebba ba ne suk haifar da ambaliyar, yana mai alaƙanta matsalar da ƙaruwar tasirin sauyin yanayi, da kuma ruwan sama da ya wuce kima.

Ya ƙara da cewa, tawagar ƙwararru daga ma’aikatarsa da kuma sauran hukumomi na garin domin auna irin ɓarnar da lamarin ya haifar.

Utsev ya buƙaci gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki su riƙa la’akari da gargaɗin da hukumomi ke fitarwa tare da aiwatar da matakan kariya.

Ya ce, “Ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar mahalli ta tarayya tana jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja, musamman al’ummomin da abin ya shafa a Mokwa, waɗanda suka fuskanci asara, mace-mace da kuma raba su da muhallansu sakamakon wannan bala’i.

“Ina so in jaddada cewa ba ruwan da aka saki daga madatsun ruwan Kainji ko Jebba ne ya haddasa ambaliya ba, kuma duk madatsun ruwan su na nan ƙalau.

“Mun yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Neja, da kananan hukumomi, da masu bayar da agajin farko waɗanda suka dukufa wajen bayar da agaji da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.

“Ambaliyar da ta afku a garin Mokwa ta samo asali ne sakamakon ruwan sama mai yawa saboda matsanancin yanayi da sauyin yanayi ke haifarwa, lamarin da ke kunno kai a duniya wanda ya mamaye magudanar ruwa na cikin gida.

“Rashin ingantattun hanyoyin da za a bi don karkatar da ruwan da ya wuce gona da iri ya ƙara dagula tasirin ambaliyar ga al’umma.

“‘Yan Nijeriya za su tuna cewa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsaftar Ruwa ta Tarayya ta Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) a cikin hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2025 (AFO), a ranar 10 ga Afrilu 2025 ta yi hasashen ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomin 19 na jihar Neja ciki har da ƙaramar hukumar Mokwa.”

Ya kuma yi tsokaci kan rahoton AFO na shekarar 2025, wanda ya nuna cewa al’ummomi 1,249 a ƙananan hukumomi 176 a cikin jihohi 33 da Abuja sun faɗa cikin yankunan da ake fama da matsalar ambaliya, yayin da al’ummomi 2,187 a ƙananan hukumomi 293 da ke cikin jihohi 31 na tarayya, ciki har da babban birnin tarayya sun faɗa cikin yankin.

Jihohin da ake fama da matsalar ambaliya sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Borno, Kuros Ribas, Delta, Ebonyi, Edo, babban birnin tarayya, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, Zamfara.

“Bari in yi amfani da wannan damar don sake maimaita muhimman gargaɗin da shawarwari daga rahoton Annual Flood Outlook (AFO) na 2025.

“Mun buƙaci kuma muna ƙara kira ga jihohi da ƙananan hukumomi da su yi aiki da waɗannan gargaɗin na farko ta hanyar: ƙarfafa ababen more rayuwa na magudanar ruwa, Matsar da al’ummomin da ba su da ƙarfi daga filayen ambaliyar ruwa, da aiwatar da ci gaba da yaƙin wayar da kan jama’a; da kuma aiwatar da ƙa’idojin amfani da filaye don hana kutsawa cikin yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa,” inji shi.

Fiye da mutum 230 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman wasu fiye da 400 bayan mummunar ambaliyar da ta auka wa garin.

By ukarofi