Matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal ka iya kai darajar kusan fam miliyan 340, idan za a sayar da shi, a cewar wata ƙungiya a ƙasar Switzerland mai nazari kan darajar ’yan wasa.
A wata ƙididdiga ta daban, cibiyar sanya idanu kan ’yan wasa ta CIES, ta ƙiyasta cewa ɗan wasan mai shekara 17 zai kai darajar euro miliyan 400 – kusan ninkin abin da aka sayar da Barcelona ta sayar da Neymar – yuro miliyan 222 – ga PSG a 2017, mafi tsada a lokacin.
Matashin ɗan Sifaniya ya kasance na biyar cikin jerin matasan ’yan ƙwallo da suka haska a kakarsu ta farko a gasar La Liga, a lokacin yana da shekara 15 da wata tara.
Ya zarta Messi da ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas – da ƙwallo 23 a daidai waɗannan shekaru.
Ga jerin ’yan wasan 10 da suka fi daraja:
1. Lamine Yamal (Barcelona) yuro miliyan 340.
2. Erling Haaland (Man City) yuro miliyan 200.
3. Jude Bellingham (Real Madrid) yuro miliyan 197.
4. Kylian Mbappe (Real Madrid) yuro miliyan 162.
5. Jamal Musiala (Bayern Munich) yuro miliyan 130.
6. Pedri (Barcelona) yuro miliyan 121.
7.Vinicius Junior (Real Madrid) yuro miliyan 109.7.
8. Cole Palmer (Chelsea) yuro miliyan 106.5.
9. Julian Alvarez (Atletico Madrid) yuro miliyan 106.
10. Florian Wirtz (Bayer Leverkusen) yuro miliyan 103.
