An naɗa Simone Inzaghi a matsayin kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafar Saudiyya ta Al-Hilal, kwana guda bayan barin Inter Milan.
Kocin na Italiya ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu bayan ya bar Inter ranar Talata.
Kulob ɗin ta Serie A ta sha kaye da ci 5-0 a wasan ƙarshe na gasar kofin zakarun Turai da suka doka ranar Asabar da Paris St-Germain, abin da ke nuna irin rashin lashe kofuna da ƙungiyar da fama da shi tun 2019-20.
Inzaghi ya karɓi ragamar horar da Inter a shekarar 2021, inda ya jagoranci Nerazzurri zuwa gasar lig ta 2023-24 kuma ya lashe Coppa Italia sau biyu.
ɗan wasan mai shekaru 49 ya kuma jagoranci Inter zuwa wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a 2023, inda ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 1-0.
Inzaghi ya gaji kocin Portugal Jorge Jesus, wanda ya jagoranci Al-Hilal a gasar kofin Saudi Pro League a 2023-24 amma an kore shi a watan da ya gabata bayan an fitar da ƙungiyarsa a gasar kofin Zakarun Turai ta Elite Semi Final.
ɗan ƙasar Italiya ya gaji tawagar da ta ƙunshi tsohon ɗan wasan baya na Manchester City Joao Cancelo da tsohon ɗan wasan Wolves Ruben Neves da tsohon ɗan wasan Fulham Aleksandar Mitrovic.
Kyaftin ɗin Manchester United Bruno Fernandes ya ƙi amincewa da tayin “mai ban sha’awa” daga Al-Hilal a wannan makon saboda yana son “wani tayinnda ya fi shi”.
Kafofin yaɗa labaran Italiya sun ruwaito cewa kwantiragin Inzaghi ya kai Yuro miliyan 30 a duk kakar wasa.
