Fulham ta sanar cewa, Willian da Carlos Vinicius za su bar ƙungiyar bayan da yarjejeniyarsu za ta ƙare a ƙarshen watan Yuni.
Willian, wanda ya sake komawa Fulham a farkon shekarar nan ya buga wasa 79 tun bayan da ya fara buga mata tamaula a 2022 a karon farko.Shi kuwa Vinicius zai yi ban kwana da Fulham, bayan da suke su uku a gurbin da yake bugawa, idan aka haɗa da Raul Jimenez da Rodrigo Muniz.
Fulham ta yi wa kyaftin ɗinta Tom Cairney tayin karin kwantiragi, wanda ake alaƙanta shi da zai koma Wrexham, wadda za ta buga gasa a baɗi.
Sauran da aka yi wa tayin tsawaita kwantiragi a Fulham sun haɗa da Kenny Tete da matashi Luc De Fougerolles da Callum Osmand da kuma Lemar.
