
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ya bayyana cewa jihar tana kewaye da ƴan ta’adda da ƴan fashi, inda hare-haren da ake kai wa a ƙauyuka a ƴan kwanakin nan sun kere tsakanin makiyaya da manoma.
An samu adadi mai yawa na hare-hare a ƴan makonnin nan a yankin Arewa ta Tsakiya, waɗanda suka jefa ƙananan hukumomi da dama cikin mawuyacin hali, lamarin da a sakamakonsa aka rasa mutane masu tarin yawa.
A yayin hira da shi ta gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Gwamna Alia ya ce ƴan ta’addar sun shirya hare-haren ne tare da ƙaddamar da su a wurare mabanbanta a jihar.
Ya ce, lallai waɗannan hare-haren sun wuce a ce na manoma da makiyaya ne kaɗai, inda ƙwararrun mayaƙa ne suke aiwatar da su.
Ya kuma ce, abin takaicin shine ba a taɓa ko ɗaya daga cikinsu ba saboda a mafi yawancin lokuta su kan kai hari ne da tsakiyar dare, inda cikin hanzari suke tserewa.
Gwamnan ya zargi wasu ƴan majalisar ƙasa da ɗaukar nauyin hare-haren da ke faruwa a Benue, yana mai cewa lallai ba za su lamunci hakan ya cigaba da aukuwa ba.
Ya kuma ce, wani rahoton da tawagar shari’a ta ke gudanarwa a jihar ya ayyana sunayen wasu manyan mutane, inda da zara an kammala shi a mako mai zuwa, za su ɗauki matakin doka a kai.
