
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Rundunar Sojoji (COAS) Janar Olufemi Oluyede ya yi kira ga dakarun atisayen ‘FANSAN YAMMA’ da su daƙile ayyukan ƴan ta’adda da ke addabar al’umma a shiyyar Arewa maso Yamma.
Janar Oluyede, wanda ya samu wakilcin Kwamandan dakarun yaƙi na zamani, Janar Adeleke Ayannuga, ya halarci taron cin abinci na musamman tare da jami’an a Sakkwato, ranar Juma’a.
Ya ce, sojoji sun yi nasarar nakasa ƴan ta’addar, inda kuma suna cigaba da ƙoƙarin tabbatar da cin galaba akansu, yana mai nuni da muhimmancin haɗa kai tsakanin sauran hukumomin tsaro domin cimma nasara.
A yayin taron ne Shugaban sojojin ya raba abinci da abin sha ga dakarun da kuma ƙoƙarin haɗa kansu wajen rera waƙoƙi da nufin ƙara musu karsashi.
Haka kuma ya ziyarci sojojin da suka samu raunuka a yayin faɗa da ƴan ta’adda a asibiti, inda a nan ma ya ƙarfafe su tare da ba su tabbacin samun goyon bayan Gwamnatin Tarayya.
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na ɗaya daga cikin masu alfarma da suka halarci taron.
Bugu da ƙari, an gudanar da wasannin gargajiya domin nishaɗantar da al’umma gami da ƙara wa sojojin karsashi a taron.
