Abinda ba a bayyana ba game da ƴan wasa 22 da suka rasu a hatsari da haihuwar iyalin ɗaya daga cikinsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yayin da ake tsaka da jimamin rashin Kanawan ƴan wasan, iyalin ɗaya daga cikin mamatan, wato Abubakar Yakubu Isma’il ta haifi ɗa namiji kwanaki shida bayan aukuwar hatsarin, wanda ya rutsa da ƴan wasa sama da 20 a lokacin da suke koma wa gida daga babban taron wasanni na ƙasa da aka yi a Jihar Ogun.

Abubakar yana ɗaya daga cikin mutane 21 da suka rasu a yayin aukuwar lamarin, inda matarsa Ummi mai ɗauke da tsohon ciki ta samu labarin a lokacin da take tsaka da yin girki.

Lamarin da ya jefa ta cikin tashin hankali da zuwa wajen da aka ajiye gawawwakin a asibitin Abdullahi Wase dake cikin garin Kano cikin baƙin ciki tare yin kuka sosai.

Daga nan ne iyalan nasu suka sake shiga damuwa duba da cewa lokacin haihuwarta ya ƙarato, inda suka kai ta wani asibitin kuɗi a Tarauni, wanda a nan ne ta haihu, ranar Asabar.

Tuni aka mayar da sunan mahaifin da ya rasu akan jaririn, kuma iyalan suka ce za a yanka masa rago a rana ta bakwai da haihuwarsa.

Wani yayan Abubakar, ya ce mamacin ya kasance likita ne a lokacin da ya ke raye, wanda ya ke tsaka da karatun digiri na uku, yana mai cewa ba za a taɓa mantawa da shi ba.

Haka kuma ya ce, mamacin ya kan sauka ne a Tashar Yari, wani gari da ake riska idan an wuce Zariya, saidai a ranar ya nemi zarcewa zuwa cikin garin Kano da nufin sayo wasu ababe, lamarin da ya sabbaba hatsarin ya rutsa da shi.

Daga bisani gwamnatin Kano ta tallafa wa iyalan kowane ɗaya daga cikin mamatan da Naira miliyan ɗaya da kuma tallafin Naira miliyan 21 daga gwamnatin Ogun domin ragewa iyalan mamatan raɗaɗi.

Sunayen mamatan sune: Nasiru Abdullahi, Aminu Muhammad, Shehu Sai’du, Usman Muhammad, Sani Yusuf, Muhammad Aminu, Hamal Dahiru, Abdurrahman Muhd, Abdul’aziz Auwalu, Nasiru Adam, Ibrahim Salisu, Bashir Bello da Imamumalik Umar.

Sauran sun haɗa da Bilal Salisu, Ashiru Shu’aibu, Abdussamad Rabiu, Abubakar Isma’il, Bello Muhd, Usaini Garba, Isah Usman Aliyu, Isah Ibrahim da kuma Abdullahi Saleh Trigger.

By Babaji