Daga HABU ƊAN SARKI, Jos
Babban ɗan kasuwar nan na garin Ɓukur a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu, kuma basarake, Ɗangiwan Dass, Makaman Kardam, kuma Ɗan’adalan Bununu, Alhaji Danjuma Idris Bala ya yi kira ga jama’a su zauna lafiya da juna, tare da girmama shugabanni a kowanne mataki, ta haka ne za a samu cigaban ƙasa da bunƙasar rayuwa.
Basaraken ya bayyana haka ne yayin isar da saƙon sa na barka da Sallah ga al’ummar musulmi, inda ya yi nuni da cewa, idan jama’a ba su haɗa kansu da shugabanninsu da wakilansu da ke tare da gwamnati ba, babu wani cigaba da za su samu na ribar dimukraɗiyya. Sai dai su ga wasu na samun moriyar gwamnati, amma kuma su an bar su a baya.
Yayin da yake ƙara zaburar da jama’a a yi koyi da sadaukarwa da miƙa wuya irin na Annabi Ibrahim da ya yi biyayya ga umarnin ubangiji na yanka ɗansa Annabi Isma’il, amma Allah ya fanshi ran annabin sa da rago, Masun Lere Alhaji Ɗanjuma Bala, ya ce yakamata masu hali a cikin jama’a su riƙa tausayawa talakawa da kyautata musu, domin damar da Allah ya ba su.
Sannan ya ja hankalin jama’a musamman waɗanda suka samu damar zuwa aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki, su cigaba da sanya ƙasar nan da Arewa da Jihar Filato cikin addu’o’in su, domin samun ɗorewar zaman lafiya da ingantaccen tsaro.
