Daga AISHA ASAS
A ranar 31 ga Mayu, jarumar Nollywood, Toyosi Etim-Effiong, ta wakilci Najeriya a babban bikin fina-finai na duniya, Cannes Film Festival da aka gudanar a Faransa. Wannan wakilci ya zo ne bayan gayyata ta musamman daga kwamitin Cannes domin gabatar da sabbin fasahohin ‘yan Afrika a duniyar nishaɗi.
Toyosi ta bayyana cewa, wannan dama ce ta musamman domin nuna fasaha da ƙwarewar matasa a Najeriya. “Na ji daɗin yadda duniya ke fara gane irin gagarumar gudunmawar da Afrika ke bayarwa, musamman Najeriya,” inji ta.
Wannan bikin, wanda ya haɗa daraktoci da jarumai daga ƙasashe fiye da 90, ya buɗe ƙofa ga tattaunawa tsakanin Toyosi da manyan masu shirya finafinai na duniya, inda suka tattauna batun haɗin gwiwa da canjin fasahar shirya fim.
