PRP za ta yi aiki tuƙuru don kawar da mulkin zalunci da ake a ƙasar nan – Abba Namatazu

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa a tsarin ƙasar nan tun 1999 kusan tafiyar jam’iyyar ɗaya ake sai dai idan lokaci ya zo sun fahimci mutane sun gane abinda ake nufi sai a sauya mata suna ta ƙarfafa wata jam’iyyar. 

Injiniya Abba Sule Namatazu mataimakin shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa mai kula da shiryar Arewa maso yamma ne ya bayyana hakan a taron da jam’iyyar ta gudanar a ranar Asabar a ɗakin taro na gidan Mumbayya.

Ya ce a baya sunan jam’iyyar dake mulkin ƙasa ita ce PDP sai aka yi bula-bula ta koma APC, mun ce jam’iyya ɗaya ce saboda daga 1999 da mulkin farar hula ya dawo, an ɗan  kwatanta zaɓuɓɓuka a ƙananan hukumomi a wancan lokacin jam’iyyu daban-daban sun sami shugabanni na ƙananan hukumomi da kansiloli.

Ya ce daga nan aka kafa ginshiƙi na ruguza tsari na jam’iyyu da yawa haka ake ta tafiya har aka kawo yanzu abinda suke so su yi irin abinda aka yi lokacin Abacha ne duk jam’iyyu su haɗu suce  sun tsayar da Tinubu shine tsarin da aka nufa.

Namatazu ya ce mutanen ƙasar nan yanzu jikinsu ya gaya musu sun san babu yadda za a yi a tsayar da jam’iyyar APC da wata jam’iyyar ta kirki ace ta kai labari, idan kuwa aka ce mutum ɗaya ne duk jam’iyyu sun haɗu sun fiitar da shi takara ruwa ta sha kenan a wajensu.

Ya ce masu kira a zo a yi haɗaka domin a kayar da APC duk cikinsu idan aka duba waye keda bambanci da APC wani ya yi Gwamna ko Minista ko ɗan majalisa ko shugaban ƙaramar hukuma ko kansila ba Tinubu ne kaɗai ya kawo ƙasar nan halin da take a ciki ba.

Ya ce duk wanda ya yi Gwamna daga 1999 ko wani muƙami su suka haɗu suka jagula da lalata ƙasar nan waɗanda suka haɗu suka lalata ne kuma zasu dawo suce wane yafi dama~dama duk  irinsu ɗaya ne.

Injiniya Abba Sule Namatazu ya ce  jam’iyyar su ta PRP ba lallai ne ta shiga cikin wannan kwamacala tasu ba dama faɗa ne ake tsakanin ɗanjuma da ɗanjummai.

Injiniya Abba Sule Namatazu mataimakin shugaban jam’iyyar PRP na kasa mai kula da shiryar Arewa maso yamma ya ce taron da suka gudanar na jam’iyyar a Kano na su  kalli halin da jam’iyyar tasu  take ciki ne da halinda ƙasa ta shiga shekaru 26 bayan dawowar mulkin farar hula.

Ya ce a matsayin  da  PRP take  daɗaɗɗiya  jam’iya.mai aƙida da kishin talaka  za tayi duk mai yiwuwa wajen haɗa kan ya’yanta da buɗe kofa mutane masu kishi da aƙida su shigo a farfaɗo da martabar ta a Kano da Arewa da ƙasa baki ɗaya.

Ya ce a yanzu shugabannin riƙo ne ke riƙe da jam’iyyar, nan gaba zasu gudanar da babban taro na masu ruwa da tsaki a samar da zaɓaɓɓun shugabanni na kowane mataki da za suyi aiki tuƙuru domin kawar da zaluncin da ake a ƙasar nan.

Taron dai ya samu halartar ɗimbin ‘ya’yan jam’iyyar maza da mata da shugabannin jam’iyyar daga jihohin Kano, Jigawa da Kaduna da wasu da suka taɓa yi mata takara a matakai daban-daban a zaɓen da ya gabata.

By ukarofi