Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce, shi ne zai jagoranci yaƙin neman zaɓen Shugaban Tinubu na 2027 a jihar Ribas.
Wike ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Litinin a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
Duk da kasancewarsa ɗan jam’iyayar PDP ne, amma yanzu Ministan Abujan a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu ɗan jam’iyyar APC.
Ana dai zargin Wike da cin dunduniyar PDP saboda gwamnatin Tinubu sai dai a kodayaushe yakan ce shi ɗan PDP ne na gani kashe ni wanda kuma ya ci ribarta.
Sannan an yi wa Wike tambaya kan ya yake kallon makomar siyasarsa a 2027.
“Ina cikin kunshin gwamnatin Tinubu kuma shin ba ka san ni ne zan jagoranci yaƙin neman zaɓensa ba a Jihar Ribas?” Ya amsa.
Sannan wani ɗan jarida daban ya tambayi Wike kan ko yana nufin zai mara wa Tinubu baya duk da kasancewarsa ɗan jam’iyayar PDP, sai ministan ya amsa da da cewa, ” “E, to dama abin a ɓoye yake?” Ya faɗa. Wannan kawai saboda na ce yankin Kudu ne Yakamata ta fidda da ɗan takarar shugaban kasa.”
“Tinubu ne zai yi nasara a Abuja a 2027.”
A yayin zaɓen 2023, Shugaba Tinubu bai yi nasara ba a Abuja, jam’iyyar LP ce ta yi nasarar (Peter Obi).
A cikin mazaɓu 6 na babban birnin tarayya Abuja, jam’iyyar LP ta samu 4, ita kuma APC ta samu 2.
a yayin wannan tattaunawa, Wike ya yi hasashen cewa Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a Abuja a 2027.
“Kamar ba ku san cewa Tinubu bai samu kaso 10% ba a zaɓen shugaban kasa da ya gabata ba a Abuja? Amma wannan karon zai samu,” ya faɗa.
“Dalilin da ya sa PDP ba za ta iya daukar mataki a kaina ba duk kuwa da ina hidimta wa APC.”
Mista Wike ya ce, bai damu da cewa PDP za su ɗauki mataki a kansa ba saboda ya amince da yi wa Tinubu aiki a gwamnatinsa.
Ministan ya ce jam’iyyar adawa ta PDP ba za ta iya ɗaukar mataki a kansa ba saboda sai da ya fara sanar da jam’iyyar cewa zai karbi mukami a gwamnatin nan kuma ba tare da sun ƙalubalance shi ba.
“Ban karbi muƙamin minista ba sai da na sanar da jam’iyya (PDP). Na rubuta wa ofishin jam’iyyar na shiyya. Na rubuta wa gwamna. Na rubuta ga shugaban jam’iyyar na ƙasa. Kuma ina ƙalubalantar kowannensu ya fito ya faɗi idan sun ce a’a ka da na karɓi muƙamin (minista),” ya faɗa.
Sannan ya ce shi bai yi mamaki ba yadda gwamnonin PDP ba su ƙalubalanci matakin da ya ɗauka na yi wa Tinubu aiki ba saboda da yawansu suna ta ƙoƙarin nema wa abokansu muƙami a gwamnatin.
“Har yanzu ni ɗan PDP ne. Na wahalta wa jam’iyyar. Ban ga wani da ya isa ya ce min, ‘Wike kai ba dan jam’iyyar PDP ba ne. Waye zai iya? Wacce gudunmowa ya bayar sama da wanda na bayar?”
Ba wannan ne karon farko ba da Wike zai mara wa Tinubu baya a maimakon dan takarar jam’iyayarsa ta PDP ba.
Bayan zaɓen cikin gida na jam’iyyar PDP, Wike ya kafa tafiyar amana da wasu gwamnoni 4 a lokacin waɗanda ba su ji daɗin abin da ya faru ba game da takarar Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na wannan lokaci, Iyorchia Ayu, kuma hakan ne ya sa ba su yi wa jam’iyyar aiki ba.
Baya ga Wike, sauran ‘yan tafiyarsa da ake kira da G5, were Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu State) Samuel Ortom (Benue), Okezie Ikpeazu (Abia) da Seyi Makinde (Oyo).
‘Yan adawar sun bukaci shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Ayu, da ya bai wa ɗan kudu damar zama shugaban jam’iyya domin a samu daidaito na shiyya-shiyya.
Dalilinsu shi ne Atiku da Ayu dukkanninsu sun fito ne daga yankin Arewa.
Wannan rikici ya daɗa tsamari ne bayan da Atiku ya ƙi daukar Wike a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Daga baya, Atiku ya yi rashin nasara a zaɓen 2023, inda ya zo na biyu da ƙuri’u 6, 984,520 bayan biyo bayan Tinubu na APC mai ƙuri’u 8, 794, 726.
Waɗancan G5 su suka janye goyon bayansu ga Atiku kuma za su jawo faduwar dan takarar jam’iyyar.
Saɓanin sauran G5 ɗin, ana ganin Wike ya taimaka wa Tinubu a lokacin zaɓe wajen samun nasara a jihar Ribas duk kuwa jam’iyyar PDP ne.
Daga baya sai Tinubu ya naɗa shi muƙamin minista wanda ake kallo a matsayin biyan bashi na irin aikin da ya yi wa Tinubu a lokacin zaɓe.
