Muna buƙatar diyya daga Gwamnatin Tarayya saboda soke hawan sallah – Gwamntin Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya diyya sakamakon soke bikin hawan Sallah na tsawon shekaru biyu a jere.

Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Tajo Uthman, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin da sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kai gaisuwar sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnati.

Uthman ya ce, jihar ta yi asarar kuɗaɗe masu yawa sakamakon dakatar da wannan biki na al’ada da ake gudanarwa a kowace shekara, wanda a kullum ke jawo baƙi daga ciki da wajen ƙasa.

“Bikin hawan sallah an amince da shi a matakin UNESCO a matsayin wani abin tarihi. A lokacin wannan biki, Kano na samun kuɗaɗen shiga masu yawa daga baƙin ƙasa da na cikin gida,” in ji shi.

Ya bayyana cewa tasirin tattalin arzikin da soke bikin ya haifar ya shafi kasafin kuɗin jihar na shekara-shekara.

Ya jaddada cewa, Gwamnatin Tarayya ya zama wajibi ta ɗauki nauyin asarar tattalin arzikin da aka fuskanta sakamakon sokewar, tare da biyan jihar diyya yadda ya kamata.

“Lokaci ya yi da za mu buƙaci diyya kan asarar da muka tafka,” in ji kwamishinan.

Sannan ya kuma buƙaci a gaggauta dawo da bikin a jihar, yana mai bayyana soke bikin a matsayin abin takaici.

By ukarofi