Wani magidanci ya yi mutuwar kasko da wani mai fakewa da sana’ar jari-bola yana yi wa mutane fashi, bayan da gungun wasu ’yan jari-bola suka yi ƙoƙarin cire tagar gidansa da ƙarfin tsiya a yankin Babban Birnin Tarayya.
Magidancin, wanda ke sana’ar sayar da tufafin gwanjo ya gamu da ajalinsa ne bayan ɓata-garin sun caka masa wuƙa a yankin Tsohuwar Kutunku da ke ƙaramar Hukumar Gwagwalada.
Wani ɗan unguwar mai suna Francis Nnamdi, ya ce da misalin ƙarfe 9.26 na dare ne wasu mutum uku masu sana’ar bola-jari suka je gidan mutumin, suna ƙoƙarin cire ƙarfen tagarsa.
Ya ce cewa bayan mai gidan ya gan su ne ya tunkare su domin jin dalilinsu na neman cire masa tagogi, inda a garin haka ɗaya daga cikinsu ya zaro wuƙa.
Ganin haka ne mutumin ya shiga daki ya ɗauko adda, kuma a garin rikicin masu bola-jarin suka caka masa wuƙa, shi kuma ya mayar da martani ta hanyar saran ɗayansu da addar hannunsa, ragowar kuma suka tsere, suka bar ɗayan kwance a cikin jini.
Ya ce daga bisani makwabta suka kira ’yan sanda, suka ɗauke gawarwakin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda likitoci suka sanar cewa dukkansu sun mutu, aka ajiye gawarwakin a ɗakin ajiye gawa.
