Wani mutum ya cinna wa kansa wuta a harabar kotu ta Aljeriya a ranar Lahadi.
Faouzi Zegout, daga garin Frenda, mai tazarar kilomita 340 daga yammacin Algiers, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka bayyana, ya watsa wa kansa man fetur a kusa da ginin gwamnati tare da cinnawa kansa wuta.
Sai dai kuma jami’an tsaro na kotun sun yi gaggawar shiga tsakani tare da kashe wutar inda mutumin ya samu ƙananan raunuka, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa AFP.
“Faouzi Zegout yana asibitin Algiers yana jinyar ƙunar da ya samu,” amma “yana samun sauƙi,” inji jaridar Frenda.
“Na cinna wa kaina wita ne saboda wani alƙali a kotun Frenda wanda ya yi min barazanar ɗaurin shekaru 10 ba bisa ƙa’ida ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, yana son jawo hankalin Shugaba Abdelmadjid Tebboune don a yi masa adalci”.
Zegout ya ce, kwanan nan ya bayyana a gaban kotu don ƙaddamar da wani tallafi ba tare da izini a hukumance ba don taimakawa wajen bayar da magani ga marasa lafiya.
A ranar Lahadi ne dai kotun za ta yanke hukuncin, a daidai lokacin da ya yi yunƙurin kashe kansa.
Ba kasafai ake yin wannan aika-aika ba a Aljeriya, saɓanin a makwabciyarta Tunisia.
