
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya shelanta cewa alaƙarsa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu tana nan da ƙarfinta sakamakon a yanzu an samu yafiya a tsakanin su.
A baya ne aka samu rahotannin da ke nuna cewa an samu tsamin dangantaka a tsakanin Shugaban Ƙasar da gwamnan, wanda yi ta yaɗawa a Soshiyal Mediya.
A watan Mayu ne Shugaba Tinubu ya yi buris da gwamnan a lokacin da ya je Legas domin ƙaddamar da zangon farkon na aikin titin Legas zuwa Kalaba.
A wani bidiyo da mataimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin Soshiyal Mediya, Dada Olusegun ya yaɗa, an ga yadda Tinubu ya je wajen da gwamnoni suke, inda ya gaisa da sauran tare da tsallake Sanwo-Olu wanda da farko ya jira shi domin su gaisa, amma hakan bai yiwu ba.
Daga bisani, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, komai ya wuce kuma ya yafe duk abin da ya shiga tsakanin su, yana mai tabbatar da cewa ba ya fushi da kowa har da gwamnan.
Hakan ya faru ne a yayin da gwamnan da wasu jagororin gwamnatinsa suka je wa Shugaban ƙasar yawon sallah a gidansa dake Ikoyi a Legas, inda Tinubu ya bayyana yafiyarsa a fili game da al’amarin.
