Borno: Sojojin NAF sun wargaza shirin Boko Haram na kai hari a Marte da Monguno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an sojojin sama (NAF) da ke aiki a ƙarƙashin atisayen HAƊIN KAI sun yi nasarar lalata shirin mayaƙan Boko Haram/ISWAP da suka yi yunƙurin kai wa a Ƙananan Hukumomin Marte da Monguno dake Jihar Borno.

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin a lokacin da mayaƙan suke gudanar da atisayen kai farmakin a yankin Bukar Meram dake Tafkin Chadi, inda sojojin suka hango su.

Daga nan ne sojojin suka far musu tare da tarwatsa wasu muggan makaman yaƙi da wajen ajiyarsu gami da wasu motoci.

Kakakin NAF, Air Kwamado Ehimen Ejodame a wata sanarwa ranar Talata, ya ce dakarun tsaron sun yi wa ƴan ta’ddar ba-zata da ruwan alburusai, lamarin da ya yi sanadin ɗaiɗaita su da lalata kayan aikinsu.

Ya bayyana cewa, hakan ya biyo bayan bayanai na sirri ne da tawagar atisayen ta samu waɗanda a sakamakon haka ne aka hallaka da dama daga cikin mayaƙan.

By Babaji