Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Alhaji Jahi Abdullahi, mai riƙe da muƙamai daban-daban na ƙungiyoyin kasuwanci a matakin Kano da arewa wanda shi ne, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa na jihohin arewa da ake kira Northern Multifarious Traders Union Of Nigeria (NOMTUN) kuma sakataren kwamitin dattawa na kasuwar Sabon Gari kuma babban sakataren na ƙungiyar yan kasuwar Sabon Gari Market Youth Traders And Deɓelopment Association (SAMYOTDA).
Har ila yau sakatare a ƙungiyar masu sanar sayar da yeri na jihar kano da ake kira Jewelries Dealers Deɓelopment Association (JEDDA) ya bayyana cewa kwanciyar hankali da suka samu na zaman su a rinfinan su na kasuwa ba tare da fargabar tashinsu ko kwace rufunan su ba wannan kwanciyar hankali da suka samu ta ishe su su ce an samu cigaba a harkar kasuwancin su saɓanin gwamnatin da ta shuɗe kullum a fargaba suke da kuma zuwa kotu har tsawan shekaru uku Allah ya basu nasara a babbar kotun ƙarshe da masu yi musu barazana to kuma tun zuwan gwamnan Kano Ahaji Abba Kabir Yusuf basu samu wannan matsala ba don haka su yan kasuwar sabon gari da sauran ‘yan kasuwa sun san an samu cigaba a Kano daga 2023 zuwa yau 2025 Abba ya canza Kano.
Haka kuma ya ƙara da cewa ga kuma samar da fitilun kan titi masu haskaka gari da fitilu da ake kira danjoji masu bada hannu a dukanin inda ake buƙatar su a titinan Kano ga kuma tsaro da zaman lafiya da daƙile muƙuwar ɗabia ta kwace waya da raunata mutane ko kashe su da sauran cigaba a fannoni rayuwa wannan ma nasara ce babba da aka samu a Kano inda kuma yayi kira ɗaukacin alumma kano da masoyan su wajen bada haɗin kai da addua domin samun nasara ta gaba domin cigaban Kano da kanawa ta kowanne fanni a cewar Alhaji Jahi Abdullahi Kano.
A ƙarshe Alhaji Jahi Abdullahi ya bayyana damuwa da takaici kan yadda hanyar asibitin masu larurrar fata da ake kira Asibitin Bela ta ke cikin wani hali na lalacewa wanda akwai buƙatar gwamna Abba da ya san wannan matsala tunda ya bibita ba sau ɗaya ba wanda hakan ce tasa aka gyara asibitin Bela to akwai buƙatar gyara asibitin Bela ta wuce har zuwa minjibir da sauran garuruwa da zai ragewa mazauna waɗannan yankuna matsaloli musamman na lalacewar wannan hanya da ta ke buƙatar agajin gwamnatin Kano da gaggawa, shi kuwa Alhaji Kabiru Dala, wani ɗan kasuwa bayan adduar zaman lafiya da ƙaruwar arziki da yayi a wannan lokaci ya buƙaci gwamna Alhaji Abba Kabir kan ya tallafawa ‘yan kasuwa da jari mai tsoka ko da bashi ne domin gina ɗan adam yafi gina gari balle wasu abubuwan da ake yin su a daji wanda ba kowa ne zai amfanesu ba.
