A cikin wani sabon firgici da ya girgiza ƙasar Ukraine da ma duniya bakiɗaya, dakarun Rasha sun kai hari mai ƙarfi ta sama a garuruwan Kyiv da Odesa, wanda ya janyo mummunan hasara ga rayuka da dukiyoyi. Wannan hari da aka kai a daren Litinin ya kasance ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a cikin shekaru uku da suka gabata.
Rahotanni daga hukumomin tsaro na Ukraine sun bayyana cewa Rasha ta harba kimanin na’urori masu sauka ba tare da matuƙi ba guda 315 da kuma makaman balistiki da na ƙasa da ƙasa zuwa sassan daban-daban na Ukraine. A cewar mazauna yankin, hare-haren sun gudana ne cikin dare, inda mutane da dama suka farka cikin firgici yayin da ƙarar fashewar makamai ke cika sararin samaniya.
A babban birnin ƙasar, Kyiv, roƙoki sun faɗo kan gine-gine na jama’a da gidaje masu hawa, tare da haifar da gobara da ta jima kafin jami’an kashe gobara su samu nasarar shawo kanta. Wani mutum guda ya rasa ransa a harin Kyiv, yayin da wasu suka samu raunuka masu tsanani.
A birnin Odesa kuwa, an kai hari kai tsaye a wani asibitin haihuwa, lamarin da ya tada hankalin al’umma. Likitoci da marasa lafiya sun gaggauta neman mafaka yayin da vangaren ginin ya rushe. An tabbatar da mutuwar mutane biyu a Odesa, ciki har da wata ma’aikaciyar lafiya, yayin da wasu da dama suka jikkata. Matar da ta haihu kwanaki biyar da suka wuce, Iryna Britkaru, ta bayyana yadda ta tsira da ɗiyarta bayan bangon ɗakin haihuwa ya rushe.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya nuna fushinsa ga wannan hari, yana mai bayyana shi a matsayin wani “yunƙuri na rusa rayuwar fararen hula da ƙoƙarin ragargazar cibiyoyin lafiyar jama’a.” Ya kuma sake jaddada kiran da yake wa ƙasashen yamma da su ƙara taimakon soja da kayan kare kai ga Ukraine.
Rundunar sojin Ukraine ta bayyana cewa, ta samu nasarar kakkaɓe mafi yawan hare-haren da Rasha ta ƙaddamar, inda aka ce an kaɓe drones 277 daga cikin 315 da aka harɓa. Duk da haka, hasarar da aka samu na rayuka da dukiya mai girma ce.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin cimma wata yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha, lamarin da ke kara dagula lamarin. ƙungiyoyin agaji da na kare haƙƙin bil’adama sun bayyana damuwarsu kan yadda fararen hula, musamman mata da yara, ke ci gaba da fuskantar illar hare-haren da ba su da alaƙa da filin yaki.
Majalisar Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar NATO sun nuna alamar goyon baya ga Ukraine, tare da sanar da shirin ƙara ɗaukar matakan takunkumi a kan Rasha da kuma bayar da ƙarin tallafi na kayan kare kai da horo.
Yanzu haka, hukumomi a Kyiɓ da Odesa na ci gaba da tantance ɓarnar da aka yi, yayin da jama’a ke ci gaba da fuskantar rayuwa cike da fargaba da tashin hankali. Tuni aka ƙaddamar da shirin agaji da kwashe waɗanda suka rasa matsuguni zuwa wasu sansanoni na wucin gadi.
