Daga
BILKISU YUSUF ALI Ph.D
Wannan wani salo ne na mayar da komai siyasa da kuma tsantsar son zuciya ne alaƙanta daba da kwacen waya da gwamnatin tarayya. Wannan ragon tunani ne na mayar da komai siyasa a Kano. Su fa yan dabar nan da kwacen waya ba ruwansu da wane ɗan NNPP ne ko wane dan APC ne , in sun fito sun yin kan me uwa da wabi ne. Rayuwar kowa na cikin hatsari a jihar don haka in za a nemi mafita kawai a nema, kuma ba iya gwamnati ba, sai iyaye sun tashi tsaye musamman mata don su suke tare da ‘ya’ya ta mutanen gari da addua ta neman ɗauki da ya shirya mana zuriya.
Sannan gwamnatin tarayya da ta jiha da masu hannu da shuni su haɗa kai su samar da wuta ko ta jihar Kano ce don a buɗe masana’antu matasanmu su samu ayyukan yi. A baya dabar ai an san iya unguwannin da suke yi amma na yanzu sun zama gidan kowa akwai amma wai ake danganta daba da Ganduje ko APC ko gwamnatin tarayya. Allah ya kare mu da kariyarsa ya raba mu da ‘yan son zuciya, amin.
