
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta yi tir da hare-haren Isra’ila akan Iran waɗanda suka haifar da yaƙar juna a tsakanin ƙasashen biyu tare da musayar wuta da makamai masu linzami.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje a Abuja, Kimiebi Imomotimi Ebienfa a wata takarda, ya yi kira da a gaggauta zama domin kawo ƙarshen faɗan da samar da zaman lafiya.
Ya ce, yaƙar juna da suke yi ba iya al’umma gama-gari ya ke shafa ba, har ma da haddasa tashin-tashina a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ka iya tasiri ga harkar tsaro a mataki na ƙasa-da-ƙasa da cigaban tattalin arziƙi.
Ya yi kira ga majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ta gaggauta tsoma baki domin ganin an daƙile cigaba da wanzuwar al’amarin.
Ya kuma ce, lallai sai an samu girmamawa da tattaunawa ta difulomasiyya tare da kiyaye dokokin ƙasa-da-ƙasa a tsakaninsu domin cimma hakan, yana mai cewa ɗaukar matakin amfani da ƙarfin soja ba zai kashe wutar yaƙin ba.
