
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani Babban Sakatare a ɗaya daga cikin ma’aikatun Jihar Gombe da wasu mutane guda huɗu sun rasu a sanadiyyar wutar lantarki da ta ja su, yayin da wasu 13 suka samu munanan raunuka a safiyar ranar Asabar.
Muhammad Yusuf Kulani ya kasance Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Haɗin kan Shiyyoyi ta jihar.
Maƙota sun ce, iftila’in ya samu Kulani ne a lokacin da ya ke ƙoƙarin buɗe babbar ƙofar gidansa da ke yankin Tudun Wadan Pantami a Birnin Gombe.
Sannan, a lokacin faruwar al’amarin, sakataren yana tare da ƴarsa, wadda a yanzu tana asibiti.
Tuni aka yi jana’izarsa tare da sauran mutane huɗun kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Rundunar ƴan sanda a jihar ta ofishin Kakakinta, DSP Buhari Abdullahi a yayin tabbatar da al’amarin, ta ce a sakamakon ƙarfi da wutar lantarki ta yi daga wani tiransfoma a kusa da yankin da abin ya faru, aka samu aukuwar iftila’in.
Ta kuma ce, za ta gudanar da bincike mai zurfi game da musabbabin faruwar al’amarin da tabbatar da adalci a kai.
Gwaman jihar, Inuwa Yahaya ya yi jimamin al’amarin da addu’ar fatan samun rahama ga mamatan, kamar yadda Kakakinsa Ismaila Uba Misilli ya bayyana a wata takarda.
